Guguwar Tinubu na Kwasar 'Yan Adawa, Karin Sanatoci, 'Yan Majalisa 12 Sun Koma APC
- Jam'iyyar APC na ci gaba da kwasar yan adawa a lokacin da ake zarginta da kokarin mayar da siyasar kasar nan kan tsayin jam'iyya daya
- ‘Yan majalisa 10 daga jihar Akwa Ibom da aka zabe su karkashin jam’iyyun PDP da YPP sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki
- Sun bi gwamnan jiharsu, Fasto Umo Eno zuwa jam'iyyar bayan ya nemi mukarrabansa dake son zama a gwamnatinsa su bi shi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – ‘Yan majalisar tarayya 10 daga jihar Akwa Ibom da aka zabe su karkashin jam’iyyun PDP da YPP sun yanke shawarar komawa APC mai mulki tare da Gwamna Umo Eno.
Wannan sauyin sheka ya zo ne bayan wasu sanatoci biyu daga jihohin Edo da Nasarawa, Neda Imasuen da Ahmed Wadada, su ma suka bayyana shirinsu na sauya sheka zuwa APC.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa wannan ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC ke kokarin janyo wasu gwamnoni hudu na PDP zuwa cikinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne a lokacin da zarge-zargen da ke cewa APC na kokarin mayar da Najeriya kasa mai jam’iyya daya tilo.
Sanatocin adawa sun koma jam'iyyar APC
Legit.ng ta ruwaito cewa ta tattaro cewa wasu daga cikin ‘yan majalisar dattijai da na wakilai daga Akwa Ibom sun tabbatar da niyyarsu ta sauya sheka zuwa APC.
Sai dai sun ki bayani a kan matakin da suka dauka, inda suka bayyana cewa akwai bukatar bin tsarin doka na majalisa kafin hakan.

Asali: Facebook
Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na kasa (Kudu maso Gabas), Dr Ijeoma Arodiogbu, ya tabbatar da cewa ‘yan majalisar na shirin sauya sheka zuwa APC.
Daga cikin ‘yan majalisar da suka mika wuya ga APC akwai:
- Sanata Ekong Sampson (Akwa Ibom ta Kudu)
- Sanata Aniekan Bassey (Akwa Ibom ta Kudu maso Gabas)
- Okpolupm Etteh ('Dan majalisar wakilai)
- Paul Asuquo
- Alphonsus Uduak
- Ime Bassey
- Martins Esin
- Unyime Idem
- Mark Esset
Har ila yau, Emmanuel Ukpongudo na jam’iyyar YPP shi ma ya bayyana kudirinsa na shiga APC.
APC na ci gaba da kwasar ‘yan adawa
Sauya shekar na zuwa kasa da mako guda bayan Gwamna Umo Eno ya sanar da barin PDP zuwa APC a ranar Juma’ar da ta gabata, yayin da a watan Afrilu Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, ya koma APC.
Gwamnan Jihar Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodimma, ne ya jagoranci tawagar da ta karɓi Gwamna Eno zuwa jam’iyyar APC.
Gwamna Eno ya ce:
“Na yanke shawarar komawa APC domin ci gaba da tafiya da sauyi. Gwamnatin mu tana tafiya ne bisa tsarin shigar kowa da kowa, kuma hakan ba zai canza ba.”
ACF ta yi tir da tallata Bola Tinubu
A baya, mun wallafa cewa dattawan Arewa sun bayyana rashin jin dadi a kan yadda wasu daga cikin yan jam'iyyar APC suka fara yiwa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kamfe.
Sakataren Yada Labaran ACF na ƙasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce yanzu ba lokacin neman kuri'a na zaben 2027 ba ne.
Kungiyar ta kara da cewa daga cikin matsalolin da suka sako Najeriya a gaba akwai faduwar darjar Naira, tabarbarewar tattalin arziki da matsanancin rashin tsaro a sassa daban-daban.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng