Hadimin Tinubu Ya Ajiye Aiki, Ya Fadi Dalilin Rabuwa da Gwamnatin APC
- Hadimin shugaba Bola Tinubu, Aliyu Audu ya sanar da murabus daga mukamin Mashawarcin shugaban kasa kan harkokin jama'a
- Aliyu Audu ya ce ya fice daga gwamnati ne domin ba zai bari a yi amfani da shi wajen mayar da Najeriya kasa mai jam’iyya daya ba
- Ya ce bai dauki matakin saboda yana da wani ra'ayi da ya zo daya da jam'iyyar adawa ta PDP ba, sai dai don kishin gaskiya da amana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Aliyu Audu, mai ba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan harkokin jama'a, ya sanar da ajiye aiki.
Ya tabbatar da haka a wasikar da ya rubuta mai dauke da kwanan wata 8 ga Yuni, 2025, wacce ya aika wa shugaban kasa ta hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila.

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Aliyu Audu ya kara da cewa wannan ajiye aiki zai fara aiki ne nan take baba tare da bata lokaci ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin Bola Tinubu ya ajiye aiki
Daily post ta wallafa cewa a takardar ajiye aikin, Aliyu ya nuna godiya matuka ga Shugaba Tinubu bisa damar da ya ba shi na yin hidima a gwamnatinsa.
Ya ce:
“Ina matukar godiya gare ka, Shugaban kasa, bisa damar da ka ba ni na yi wa wannan kasa hidima karkashin jagorancinka mai hangen nesa. Abin alfahari ne a gare ni in taka rawa wajen yada manufofin wannan gwamnati.”
Audu ya kuma gode wa tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, wanda ya ba da sunansa don nada shi mukamin da ya ajiye.
Dalilin hadimin Tinubu na murabus
A cikin wata sanarwa da ya fitar daga baya kan dalilin murabus dinsa, Aliyu Audu ya ce ya yanke wannan shawara ne saboda tsayawa bisa gaskiya ba don yiwa gwamnati tawaye ba.

Asali: Facebook
Ya ce:
"Na ga maganganu da dama dangane da murabus dina, amma ina so in fayyace cewa ba tawaye bane, sai dai saboda tsayawa a kan gaskiya."
“Ko da yake ba ni da ra'ayi daya da jam’iyyar PDP, amma na ki amincewa a yi amfani da ni kai tsaye ko da dabara wajen mayar da Najeriya kasa mai jam’iyya daya. Wannan zai kasance cin amanar ni’imar Allah da kuma dokokin dimokradiyya.
“Duba da irin albarkar da Allah ya yi wa Najeriya musamman a wannan lokaci, wajibi ne a gare mu mu kare adalci, daidaito, da ‘yanci."
An nada Aliyu Audu ne a ranar 26 ga Agusta, 2023, a matsayin mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin jama'a, Tinubu ya amince da nadin nasa a hukumance a ranar 9 ga Oktoba, 2023.
Babban hadimin Tinubu ya ajiye aiki
A wani labarin, mun wallafa cewa Ajuri Ngelale, mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu, ya sanar da murabus dinsa daga mukaminsa a ranar Asabar, 7 ga Satumba, 2024.
A cikin sanarwar da ya fitar, Ngelale ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne domin mayar da hankali kan lafiyar iyalansa da wasu matsalolin da suka taso.
Ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Femi Gbajabiamila, a ranar Juma’a, 6 ga Satumba, 2024, amma wasu sun danganta ajiye aikin da gazawar gwamnati.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng