'Komai Ku Faɗa: Tinubu Ya Faɗi Abin da Zai Yi Wa Ƴan Najeriya, Ya Tabo Maganar Tsaro

'Komai Ku Faɗa: Tinubu Ya Faɗi Abin da Zai Yi Wa Ƴan Najeriya, Ya Tabo Maganar Tsaro

  • Bola Tinubu ya shawarci jami'an tsaro kada su tsangwami masu sukar gwamnatinsa yana mai cewa dimokuradiyya tana bukatar yanci
  • Tinubu ya ce kowane suna za a kira shi zai ci gaba da kare yancin albarkacin baki na yan Najeriya ba tare da matsala ba
  • Ya kuma shawarci jami'an tsaro da su toshe kunnuwansu yayin da suke gudanar da ayyukansu na yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan masu sukar gwamnatinsa inda ya ce ba zai kashe masa guiwa ba.

Tinubu ya shawarci hukumomin tsaro da kada su tsangwami ’yan kasa saboda suka, yana mai jaddada kare yancin fadar albarkacin baki.

Tinubu ya shawarci yan Najeriya kan tsaro
Tinubu ya sha alwashin kawo sauyi a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Facebook

Tinubu ya shawarci jami'an tsaro kan ayyukansu

Yayin jawabin ranar dimokuradiyya a Majalisar Tarayya da ke Abuja, Tinubu ya ce za su ci gaba da bari a yi suka koda kuwa ba daɗi, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce ko kadan bai kamata a bari kalaman wasu mutane ya raunana guiwar jami'an tsaro ko muƙarraban gwamnati ba.

Ya ce:

“Kada ku ji tsoro in an fadi kalmomi marasa daɗi a kanku.”
“Wasu shawarwari mafi kyau ga ɗan siyasa na iya zuwa daga abokan gaba idan suna da hangen nesa mai kyau.
“Ba ma neman a yi shiru, domin tursasa mutane yin shiru yana haifar da rudani da kiyayya, ba dimokuradiyya ba a karshe.”
“Duk da cewa sharrin ƙarya da bata suna bai kamata a yi shiru ba, kada a azabtar da mutum saboda rubuta rahoto mara daɗi.”
Tinubu ya bugi kirji kan salon mulkinsa
Tinubu ya karfafi jami'an tsaro kan ayyukansu. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Twitter

Rokon da Tinubu ya yi ga yan Najeriya

Tinubu ya bukaci karin hakuri inda ya ce dimukraɗiyya na bukatar lokaci da hakuri daga yan kasa, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa:

"Dimokuradiyya na bukatar haƙuri da fushin mutane da kalamai masu zafi.”
“Ku kira ni kowanne suna. Ba na nan domin na faranta muku rai a siyasa kuma zan ci gaba da kare hakkinku.”

Tinubu ya bukaci ‘yan majalisa su fifita tattaunawa fiye da danniya, su fifita haƙuri fiye da ƙarfin iko a ayyukan majalisa.

Ya ce:

“Mu koyi fifita tattaunawa fiye da danniya, da haƙuri fiye da ƙarfi, da kare haƙƙin jama'a fiye da danniya.
“Ƙasarmu ba cikakkiya ba ce, amma tana da ƙarfi. Dimokuradiyyarmu ba mara rauni ba ce, amma tana da rai.
“Wannan yana nufin burinmu na samun ƙasa mai arziki da farin ciki har yanzu yana hannunmu kuma yana da amfani mu yi ƙoƙari."

Tinubu ya karrama yan Najeriya da lambar yabo

Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya ba marigayiya Kudirat Abiola, Janar Shehu Musa Yar’Adua da Farfesa Humphrey Nwosu lambar yabo.

Wole Soyinka da Janar Akinrinade sun samu lambar yabon GCON, yayin da Bola Ige, Balarabe Musa da sauransu suka samu CFR.

Tinubu ya ce za a saki cikakken jerin waɗanda aka karrama nan gaba, ciki har da sababbin sunaye da suka taimaka wa ci gaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.