Sukar Tinubu: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Wa Ministan Buhari Wankin Babban Bargo

Sukar Tinubu: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Wa Ministan Buhari Wankin Babban Bargo

  • Fadar shugaban ƙasan Najeriya ta fito ta yi kalamai masu kaushi kan tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi
  • Mai ba shugaban ƙasa shawara, Daniel Bwala, ya bayyana kalaman Amaechi a matsayin waɗanda aka yi ba da zuciya ɗaya ba
  • Ya zargi tsohon ministan da nuna rashin gaskiya kan abubuwan da ya faɗa da kuma kwaɗayin ganin ya samu mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta yi martani kan kalaman da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi a kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana kalaman na Amaechi a matsayin abin da ya samo asali daga ƙarancin haƙuri da ƙwadayin mulki, maimakon damuwa da halin da ƴan Najeriya ke ciki.

Fadar shugaban kasa ta soki Rotimi Amaechi
Fadar shugaban kasa ta caccaki Amaechi Hoto: @ChibuikeAmaechi, @DOlusegun
Asali: Twitter

Mai ba shugaban ƙasa shawara ta musamman kan harkokin yaɗa manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daniel Bwala ya bayyana cewa kalaman Amaechi ba su da wani sahihanci ko damuwa da al’ummar ƙasa.

Amaechi, ya bayyana cewa dole ne a ƙalubalanci Bola Tinubu, kuma a ƙarshe a cire shi daga mulki idan har Najeriya na da burin fita daga matsanancin halin tattalin arziƙi da take ciki.

Amaechi ya kuma nuna yiwuwar kafa sabuwar haɗakar ƴan adawa da nufin “ceto ƙasar.”

Me fadar shugaban ƙasa ta ce kan Amaechi?

Amma Bwala ya yi watsi da waɗannan kalamai, yana mai kiran su da rashin gaskiya da son kai, tare da zargin Amaechi da amfani da ƙalubalen ƙasa don cimma muradun kansa na siyasa.

"Ƙoƙarin Amaechi na kai farmaki kan Tinubu yana nuna cewa ba batun manufofi bane, na ƙashin kai ne. Idan kana son nazari kan manufofi da matsaloli, to ya kamata zuciyarka ta kasance a buɗe."
"Idan Tinubu ya warware matsalolin ƙasa, ya ci gaba da mulki. Idan bai yi ba, masu zaɓe za su yanke hukunci. Mun shafe shekara biyu kacal a mulki."

- Daniel Bwala

Lauyan ya kuma bayyana cewa ana iya tantance gaskiyar Amaechi bisa ga abubuwan da ya aikata da kuma burinsa a baya.

“Ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a APC yana kan kujerar minista, amma ya sha kaye a hannun Tinubu. Tun daga lokacin ya daina shiga harkokin jam’iyya."
"Idan yana da gaskiya kan damuwarsa da makomar Najeriya, ya kamata ya goyi bayan ɗan takarar jam’iyyar bayan zaɓen fidda gwani. Amma yadda bai yi hakan ba, yana nuni da cewa batun kansa ne, ba batun jama’a ba."

- Daniel Bwala

An yi wa Amaechi raga-raga kan jin yunwa

Mai ba shugaban ƙasan shawara ya kuma ƙalubalanci iƙirarin Amaechi na cewa yana fama da yunwa.

"Mutumin da ya taɓa zama kakakin majalisa, gwamna har sau biyu, sannan minista mai ƙarfi, idan bayan shekara biyu da barin ofis yana cewa yunwa ke damunsa, to ko dai bai sarrafa dukiyar da ya samu yadda ya kamata ba, ko kuma yana ƙoƙarin yaudarar ƴan ƙasa."

"Wannan kaɗai ya isa ya hana a amince da shi a matsayin wanda zai iya shugabantar ƙasa."

- Daniel Bwala

An kalubalanci Rotimi Amaechi
Fadar shugaban kasa ta ce kwadayin mulki ke damun Amaechi Hoto: @ChibuikeAmaechi
Asali: Facebook

Bwala ya ƙara da cewa, shuwagabanni masu damuwa da talakawa na nuna hakan ne a aikace, ba kawai ta magana ba.

“Lokacin da ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa, shin ya ziyarci sansanonin ƴan gudun hijira ko matalauta kamar yadda yake cewa yana faɗa don su?"
"A’a. Maimakon haka, ya tara abokan siyasa domin shirya yadda za su hambarar da shugaban ƙasa mai ci. Wannan ya bayyana komai."

- Daniel Bwala

Amaechi ya taɓo batun takara a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan batun ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ba zai cire yiwuwar fafatawa da Shugaba Bola Tinubu ba a zaɓen 2027.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana cewa har yanzu yana ji a jikinsa cewa akwai gudunmawar da zai iya badawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng