'Laifinka ne': Tsohon Minista Ya Soki Gwamnan Plateau kan Karbar Jakadan Isra'ila
- Tsohon Ministan Najeriya, Femi Fani-Kayode ya soki Gwamna Caleb Mutfwang, kan karɓar Jakadan Isra’ila a Plateau
- Fani-Kayode ya bayyana taron a matsayin kuskure mai girma, yana zargin Isra’ila da cin zarafin addinai da kuma tayar da hankali
- 'Dan siyasar ya ce karɓar wakilin Isra’ila na iya jawo matsaloli ga gwamnati da kuma ƙara ta da tarzoma a cikin ƙasar nan
- Ya kuma danganta lamarin da cin zarafin Falasɗinu da ƴan Yahudun Habasha, yana ganin hakan abin kunya ne ga Kiristoci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeriya, Cif Femi Fani-Kayode ya caccaki Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau.
Fani-Kayode ya soki gwamnan bisa karɓar Jakadan Isra’ila, Michael Freeman a kwanakin baya.

Asali: Facebook
Fani-Kayode ya bayyana haka a jiya Litinin 21 ga watan Afrilun 2025 a shafinsa na X kan matsalolin tsaron jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan majalisa ya dauki zafi kan hare-haren Plateau
Hakan ya biyo bayan zargin jami'an tsaro da wani dan majalisar wakilai ya yi a jihar Plateau yayin da jihar ke fama da hare-hare.
'Dan majalisa da ke Bassa/Jos ta Arewa a majalisar wakilai, Daniel Asama, ya zargi jami’an tsaro da cewa suna da bayanai game da masu kai hari Plateau .
Asama ya bayyana cewa kisan gillar da ake ci gaba da yi a wasu sassan Plateau na da kamanceceniya da yunkurin karbe ƙasa daga hannun mutanen yankin.
An ce zuwa yanzu, mutane kimanin 100 ne suka rasa rayukansu cikin makonni biyu sakamakon hare-haren da ba su lafa ba a jihar, wasu da dama sun rasa muhalli.

Asali: Facebook
Rashin tsaro: Fani-Kayode ya soki gwamnan Plateau
Fani-Kayode ya ce karɓar jakadan Isra’ila ya sabawa dabi’un Kiristoci da kishin Najeriya baki ɗaya.
Ya zargi Isra’ila da zama ƙasa mai nuna wariyar ƙabila da addini, yana mai tambayar dalilin karɓar wakilan da ke tayar da hankali.
A cikin rubutunsa ya ce:
“Ina tambaya, a matsayina na Kirista, ya ya Gwamna Mutfwang zai karɓi waɗanda ke kashe mutane da kiyayya?
“Karɓar wakilan gwamnatin da ba ta da tausayi ba zai kawo mafita ba, sai dai ya ƙara lalata lamura.”
Fani-Kayode ya yi gargadin cewa irin wannan mu’amala na iya jawo sakamako mai tsanani ga jihar Plateau da shugabanninta a addini da siyasa.
Lamarin ya sake kunno wutar muhawara kan yadda Najeriya ke gudanar da dangantakar da ƙasashen ƙetare, musamman game da rikicin Isra’ila da Falasɗinu.
Gwamna ya koka kan matsalar tsaro a Plateau
A baya, kun ji cewa Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang ya bayyana damuwa kan matsalar tsaro da ta addabi jihar tun tuni.
Gwamnan ya ce tun bayan komawar Najeriya zuwa mulkin dimokuraɗiyya jiharsa ke fama da rikici wanda har yanzu bai kare ba.
Ya ce hare-hare da tashe-tashen hankula sun zama ruwan dare a jihar, inda kowane yanki ke fama da irin nasa rikicin.
Asali: Legit.ng