Abu Ya Girma: APC Za Ta Maka PDP a Kotu kan Zargin Bello Matawalle

Abu Ya Girma: APC Za Ta Maka PDP a Kotu kan Zargin Bello Matawalle

  • Jam'iyyar APC ta nuna rashin jin daɗinta kan zargin da wani jami'in gwamnatin Dauda Lawal ya yi a kan Bello Matawalle
  • APC ta bayyana cewa za ta ɗauki matakan shari'a a kan PDP saboda zargin da aka yi wa Matawalle na hannu a matsalar rashin tsaro
  • Ta bayyana cewa babu komai a cikin zargin tsabagen ƙarya da yunƙurin ɓata sunan tsohon gwamnan na jihar Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara, ba ta ji daɗin kalaman da aka yi kan tsohon Gwamna Bello Matawalle ba dangane da rashin tsaro.

Jam'iyyar APC ta yi barazanar ɗaukar matakin shari’a a kan PDP bisa zargin cewa ƙaramin ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle, yana da hannu a wasu hare-haren satar mutane da suka faru a jihar.

APC za ta maka PDP a kotu a Zamfara
Zargin Matawalle ya sa APC za ta maka PDP kotu a Zamfara Hoto: Dauda Lawal, Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar APC, Yusuf Idris Gusau, ya fitar ranar Laraba, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta soki ikirarin da Mustapha Jafaru Kaura, mai taimakawa Gwamna Dauda Lawal kan harkokin yaɗa labarai, ya yi.

APC ta ƙaryata zarge-zarge kan Bello Matawalle

Jam’iyyar ta bayyana zargin a matsayin ƙarya, ɓatanci, wanda yake cike da siyasa a cikinsa, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Sanarwar ta fito ne bayan wani taron gaggawa na kwamitin gudanarwa na jiha (SWC) na APC, ƙarƙashin jagorancin Hon. Tukur Umar Danfulani, inda aka tattauna kan kalaman waɗanda suka fito daga bakin Mustapha Jafaru Kaura.

"Ƙaryar da gwamnatin jihar Zamfara ke yaɗawa, musamman a kan Dr. Bello Mohammed Matawalle, ba wai kawai ɓatanci ba ne, dole ne sai an bincike su."

- Yusuf Idris Gusau

APC ta bayyana kalaman Kaura, musamman a wata tattaunawa da ya yi, a matsayin ƙoƙarin ɓata suna da kuma cin mutunci kai tsaye ga manyan shugabannin jam’iyyar, ciki har da Matawalle da tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari.

Sanarwar ta ƙara da cewa Kaura ya yi iƙirarin ƙarya cewa satar ɗalibai fiye da 300 daga GSSS Kankara, a jihar Katsina ranar 11 ga Disamba, 2020, ta kasance sakamakon wani haɗin baki da ya haɗa da Matawalle.

Har ila yau, ya zargi Matawalle da karɓar N300m daga tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari don a saki ɗaliban, amma ya bai wa masu garkuwa da su N30m kacal.

APC za ta shigar da PDP kara kan zargin Matawalle
APC ta musanta zarge-zagen da ake yi kan Matawalle Hoto: Dr. Bello Matawalle
Asali: Original

Jam'iyyar APC za ta garzaya kotu

“Jam’iyyar APC, wadda ta tsaya tsayin daka wajen yaƙi da ƴan bindiga a lokacin mulkin Matawalle, tana kallon wanda ƙaryar da Kaura ke yaɗawa cike da damuwa kuma ta umarci lauyoyinta su ɗauki matakin shari’a."
"Dole ne Kaura ya gabatar da hujjoji don kare waɗannan zarge-zarge masu nauyi, musamman dangane da satar ɗaliban Kankara a shekarar 2020 da sauran zarge-zargen satar mutane da aka ce an shirya su tun da farko.”

- Yusuf Idris Gusau

Matawalle ya ba Gwamna Dauda shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ba gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, shawara.

Bello Matawalle ya buƙaci Dauda Lawal da ya fice daga jam'iyyarsa ta PDP domin dawowa APC mai mulki a Najeriya.

Shawarar da Bello Matawalle ya ba Dauda Lawal na zuwa ne bayan gwamnan ya fito ya bayyana cewa bai da shirin komawa jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng