Bayan Rasa Damarsa a June 12, an Gano 'Dalilin' Ƙin Dawo da Fubara Mulki a Rivers

Bayan Rasa Damarsa a June 12, an Gano 'Dalilin' Ƙin Dawo da Fubara Mulki a Rivers

  • Ranar 12 ga Yuni, magoya bayan dakataccen Gwamna Siminalayi Fubara sun yi fatan dawowarsa, amma hakan ya fuskanci cikas
  • An bayyana cewa Bola Tinubu ya shirya dawo da Fubara, amma wasu magoya baya ya fusata sansanin Nyesom Wike
  • Wike yana son ci gaba da rike mulkin Rivers don cika burinsa na siyasar 2027, tare da hamayya daga Gwamna Seyi Makinde na Oyo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Miliyoyin jama’ar Rivers, musamman magoya bayan Gwamna Siminalayi Fubara, ranar 12 ga Yuni, sun shiga bakin ciki bayan fatan dawowarsa ya dusashe.

Kowa na tsammanin Bola Tinubu zai yi amfani da ranar wajen dawo da duka hukumomin demokradiyya da aka dakatar a watan Maris.

Matsalolin da suka hana dawo da Fubara
An gano dalilin kin dawo da Fubara a Rivers. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

An yi hasashen dawo da Fubara

Dakatar da Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu da Majalisar Jiha ta biyo bayan rikicin siyasa tsakanin Fubara da bangaren Wike, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma Shugaba Tinubu ya dakile rikicin da matakin ayyana dokar ta-baci wanda ya haifar da dakatar da shugabannin jihar da duka hukumomi.

Wasu sun yi hasashen cewa Tinubu zai dawo da Fubara a ranar 29 ga Mayu ko ranar 12 ga Yuni saboda matsayin sa na demokradiyya.

Tambayar da ake yi ita ce me ya hana Shugaban kasa dawowa da Fubara ranar 12 ga Yuni da dawo da jihar bisa turbar demokradiyya.?

Saboda matsin lamba daga manyan 'yan Najeriya da yiwuwar illa ga sunansa, an ce Tinubu ya shirya dawo da Fubara ko wane irin hali.

Ganawar da aka yi tsakanin Tinubu da Fubara

Tarukan da aka yi a London da gidan Tinubu da ke Legas an dauke su a matsayin alamar shirin dawo da Gwamna Fubara.

Amma wasu majiyoyi sun ce magoya bayan Fubara sun fara murna da wuri, tun kafin ranar 12 ga Yuni ta iso, cewar rahoton The Nation.

Wannan farin ciki ya fusata sansanin Wike, wanda ya dauki mataki don ganin an hana cire dakatarwar har sai an cika yarjejeniya.

Wata majiya ta bayyana cewa Fubara ma bai boye wannan shiri ba, inda ya furta a fili cewa za su dawo cikin gwamnati nan ba da jimawa ba.

Daya daga cikin sharudan sulhu da aka tattauna a London shi ne Fubara ya bar PDP kamar yadda gwamnonin Delta da Akwa Ibom suka yi.

Damar dawo da Fubara ta kubuce a ranar dimukraɗiyya
Ana zargin Wike da hana dawo da Fubara mulki a Rivers. Hoto: Nyesom Wike, Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Twitter

Abin da Wike ya ce kan Fubara

A wata hirar kafar yada labarai, Wike ya ce Fubara bai da sha’awar sulhu na gaskiya domin warware rikicin jihar.

Wike ya ce bayan Fubara ya kai masa ziyara a Abuja da wasu manyan 'yan siyasa, bai sake ganinsa ba har zuwa yanzu.

“Yana da doya. Yana da wuka. Idan kana son sulhu na gaskiya, za mu sani. Idan ba ka so, shikenan."

- Cewar Wike

Amma washegari, an ga Fubara a shafukan sada zumunta yana daukar hoto da Tinubu yayin ziyarar Bourdillon a bikin Sallah.

A cewar majiyoyi, hakan yana nuna kokarin dawo da siyasar jihar karkashin ikon Wike don shirye-shiryen zaben 2027.

Wike ya bayyana a Abuja cewa zai jagoranci yakin neman zaben Tinubu na wa’adi na biyu a 2027.

Wike yana rikici da jam’iyyarsa ta PDP tun shekarar 2023, duk da cewa Fubara na zargin goyon bayan Tinubu.

Amma har yanzu ba a san tsarin siyasa ko jam’iyyar da Fubara zai yi amfani da ita don tallafa wa Tinubu ba.

An roki Tinubu ya dawo da Fubara

Kun ji cewa jigon PDP ya bukaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya yafewa Siminalayi Fubara kamar yadda ya yafewa Babajide Sanwo-Olu a Legas.

Cif Bode George ya ce maido da Fubara zai nuna girmamawa ga waɗanda suka yi sadaukarwa don assasa dimokuraɗiyya a Najeriya.

A ranar 18 ga Maris ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Ribas tare da dakatar da gwamna, Fubara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.