Korafi Ya Biyo bayan Karramawar da Tinubu Ya Yi wa Mutane 72 a Najeriya

Korafi Ya Biyo bayan Karramawar da Tinubu Ya Yi wa Mutane 72 a Najeriya

  • Bola Tinubu ya karrama wasu fitattun jaruman da suka taka rawa a gwagwarmayar 12 ga Yuni, tare da yafewa mutanen Ogoni da aka kashe a mulkin soja
  • Kungiyoyi da mutane sun yi maraba da wannan mataki, sai dai an yi suka kan barin wasu sunaye da suka taka muhimmiyar rawa a lokacin
  • Mutanen da aka karrama sun hada da Wole Soyinka, Femi Falana, Shehu Sani da yayin da MOSOP ta bukaci a wanke sunan Ken Saro-Wiwa daga zargin kisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A ranar Dimokuraɗiyya, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana jerin sunayen wadanda aka karrama bisa rawar da suka taka a gwagwarmayar dawo da mulkin farar hula.

An bayyana cewa Tinubu ya karrama mutanen ne saboda tsayuwa da gwagwarmaya da suka yi bayan rushe zabukan 12 ga Yuni, 1993 da gwamnatin soja ta yi.

An yi martani kan karrama mutane da Tinubu ya yi
Kungiyoyi sun yi martani kan mutanen da Tinubu ya karrama. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta yi wani rahoto kan yadda kungiyoyi da sauran mutane suka yi martani kan karrama 'yan gwagwarmaya 72 da aka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda aka karrama akwai marigayi MKO Abiola, wanda aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben.

Tinubu ya kuma yi da afuwa ga mutanen Ogoni tara da suka hada da Ken Saro-Wiwa da aka kashe a 1995.

Sai dai karramawar ta haifar da martani daban-daban, inda wasu suka yaba, wasu kuma suka koka kan rashin hada wasu jaruman Arewacin Najeriya da suka yi fice a wancan lokacin.

MOSOP ta bukaci a wanke Ken Saro-Wiwa

Kungiyar kare hakkin ‘yan Ogoni (MOSOP) ta yaba da afuwar da Tinubu ya yi ga mutanenta, tana mai cewa wann an babban mataki ne na tarihi.

Amma cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Fegalo Nsuke, ya fitar, ya ce ba afuwa suke bukata ba, illa a wanke su daga zargin kisa domin ba su aikata laifi ba.

Ya ce:

“Yana da muhimmanci a tabbatar da adalci ta hanyar wanke sunayensu, domin su ci gaba da kasancewa jaruman gwagwarmaya ba tare da wani tabo ba.”

Ohanaeze ta bukaci a sa wa INEC sunan Nwosu

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yi maraba da karrama Farfesa Humphrey Nwosu, wanda ya jagoranci zaben 12 ga Yuni da lambar CON.

Rahotanni sun nuna cewa kungiyar ta ce ko da yake karramawar ta zo a makare, amma ana godiya da hakan.

Sakataren yaɗa labarai na Ohanaeze, Dr Ezechi Chukwu, ya ce:

“Ya kamata a ƙara daukar matakin tarihi ta hanyar kiran hedikwatar INEC da sunan Farfesa Nwosu.”

Korafi kan gidan rediyon Kudirat Abiola

Tsohon gwamnan Ekiti kuma dan gwagwarmayar 12 ga Yuni, Kayode Fayemi, ya bayyana rashin jin dadinsa kan rashin karrama ‘yan gidan Rediyon Kudirat.

Tsohon gwamnan ya ce 'yan gidan radiyon su suka taka muhimmiyar rawa kan dimokuradiyya a wancan lokacin.

The Guardian ta wallafa cewa ya ce:

“Ni na jagoranci aikin, amma akwai mutane da dama da suka hada kai da ni da suka ba da rayuwarsu. Yau babu wanda aka ambata daga cikinsu.”
Fayemi ya ce ba a karrama wasu jarumai ba.
Tsohon gwamna ya koka kan karrama mutane da Tinubu ya yi. Hoto: Kayode Fayemi
Asali: Facebook

'Yan adawa sun yi martani ga Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa yan adawa a Najeriya sun yi wa Bola Tinubu martani kan jawabin ranar dimokuradiyya.

Atiku Abubakar, Peter Obi da manyan jam'iyyun adawa sun ce Bola Tinubu da APC za su gane kuskurensu a 2027.

A jawabin da Bola Tinubu ya yi a ranar dimokuradiyya ya ce yana jin dadin yadda jam'iyyun adawa suka shiga rudani a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng