Dakatar da Fubara: Jonathan da Tsofaffin Shugabannin Kasa 2 da suka Taso Tinubu a Gaba

Dakatar da Fubara: Jonathan da Tsofaffin Shugabannin Kasa 2 da suka Taso Tinubu a Gaba

  • Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan na matsa wa Bola Tinubu lamba don dawo da Gwamna Sim Fubara kafin ranar dimokuradiyya
  • Majiyoyi sun ce Jonathan ne ya jagoranci ganawar sirri da Tinubu tare da umartar Fubara ya kai masa ziyarce-ziyarce
  • Ana sa ran Tinubu zai yi jawabi a Ranar Dimokuradiyya, yayin da ake fatan zai sassauta hukuncin dakatar da Fubara da mukarrabansa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu na fuskantar matsin lamba daga tsoffin shugabannin kasa kan yiwuwar maido da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.

Wata majiya ta bayyana cewa tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan da wasu shugabanni biyu ne ke matsa masa lamba don dawo da Fubara kafin 12 ga Yuni.

Jonathan ya taso Tinubu kan dokar ta baci a Rivers
Jonathan da wasu sun taso Tinubu a gaba kan dokar ta baci a Rivers. Hoto: Sir Sim Fubara, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Kokarin Jonathan a neman dawo da Fubara

Rahoton Vanguard ya ce tsohon shugaban ya kuma shirya ziyarce-ziyarce biyu da Fubara ya kai wa Tinubu a baya don tabbatar da wannan manufar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Shugaban kasar ne ke jagorantar kokarin wasu tsoffin shugabanni don matsa wa Tinubu lamba ya dawo da Fubara kafin 12 ga Yuni

An ce Jonathan ya yi doguwar tattaunawa ta waya da Tinubu, inda ya bukace shi ya dawo da Fubara kafin 12 ga Yuni don girmama dimokuradiyya.

Bisa ga wasu majiyoyi da dama an tabbatar da kokarin tsofaffin shugabanni uku na matsa wa Tinubu lamba don dawo da Fubara.

Masu sukar shugaban kasa sun danganta sassan 305 da 188 na kundin tsarin mulki da ke nuna cewa ba za a dakatar da gwamna ba ko da an ayyana dokar ta baci.

Ana rokon Tinubu ya dawo da Fubara
An bukaci Tinubu ya janye dokar ta baci a Rivers. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Facebook

Lokacin da ake hasashen dawo da Fubara

Duk da wadannan hujjoji, Tinubu ya dakatar da Fubara, mataimakinsa da 'yan majalisa masu rinjaye da ke biyayya ga Nyesom Wike, tsohon gwamna kuma ministan Abuja.

Akwai rade-radin cewa Tinubu zai janye dakatarwar a ranar 29 ga Mayu, lokacin da ya cika shekaru biyu a mulki, amma hakan bai faru ba.

Duk da haka, wasu manyan mutane daga waje na cigaba da matsa masa lamba, koda yake ba su cikin manyan masu rikici a lamarin siyasar jihar.

Majiyar ta kara da cewa:

"Baya ga Jonathan, akwai wasu tsofaffin shugabanni biyu da suka nuna damuwa kan lamarin kuma suna goyon bayan dawo da Fubara."

Bisa ga majiyoyi, ziyarce-ziyarce biyu da Fubara ya kai wa Tinubu sun kasance sakamakon umarnin sirri daga tsofaffin shugabannin, suna fatan a dawo da shi kafin lokaci.

Hakanan, alamu na nuna Tinubu cewa akwai yiwuwar a dawo da Fubara kafin cikar watanni shida da shugaban ya ambata a baya.

Wike ya koka da butulcin Fubara

Kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kuma yin magana game da rigimarsa da Gwamna Siminalayi Fubara a Rivers.

Wike ya ce yana kuka duk lokacin da ya tuna yadda Fubara ya ci amanarsa duk da taimakon da ya yi masa a siyasa.

Wike ya ce shi ya dauki nauyin Fubara, ya ba shi abinci da goyon baya, amma daga baya ya zama daga cikin abokan gabansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.