Ana Fargabar Lakurawa Sun Kashe Sojojin Najeriya 7 a Harin Kwanton Bauna a Sokoto

Ana Fargabar Lakurawa Sun Kashe Sojojin Najeriya 7 a Harin Kwanton Bauna a Sokoto

  • Ana zargin mayaƙan Lakurawa sun kashe akalla sojoji bakwai da wani farar hula a harin kwanton bauna a jihar Sokoto
  • Lamarin ya faru ne bayan dakarun Operation Fasan Yamma sun kai samame sansanin ‘yan ta’addan a Illela suna komawa sansaninsu
  • An ce maharan sun kai harin kwanton baunar ne yayin da wata motar soja ta samu matsala a hanya, kuma sojojin suka tsaya gyarawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Sokoto - Ana fargabar cewa akalla sojoji bakwai da wani farar hula sun rasa rayukansu bayan wasu da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne sun kai harin kwanton bauna a jihar Sokoto.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a kauyen Runji da ke karamar hukumar Illela a yammacin ranar Asabar.

Lakurawa sun kashe sojojin Najeriya a Sokoto
Sojojin Najeriya da ke aikin kakkabe 'yan ta'adda a dajin Sambisa. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Lakurawa sun farmaki sojoji a Sokoto

Kara karanta wannan

"Ku tashi tsaye ku kare kan ku daga ƴan bindiga," Hadimin Tinubu ga ƴan Najeriya

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa dakarun Operation Fasan Yamma na dawowa ne daga wani samame da suka kai sansanin Lakurawa da ke kusa da iyakar Najeriya lokacin da aka kai musu harin.

Majiyoyi sun bayyana cewa tun farko sojojin sun kai hari sansanin ‘yan ta’addan da motocin soja uku tare da yi musu barna mai yawa.

Wata majiya da ta san yadda aikin ya gudana ta ce daya daga cikin motocin sojin ta samu matsalar inji yayin da suke komawa sansaninsu da ke Illela.

Hakan ya sa wasu daga cikin sojojin suka tsaya domin gyaran motar kafin maharan su kai musu farmaki.

“Da alama ‘yan ta’addan sun sake haduwa bayan harin da aka kai musu sannan suka bi sawun sojojin domin daukar fansa,” cewar majiyar.

An ce maharan sun iso ne a kan kusan babura 30 dauke da mayaka masu dauke da makamai.

An yi musayar wuta mai tsanani

Majiyar ta ce an yi musayar wuta mai tsanani tsakanin sojojin da maharan bayan sun hadu a wurin da ake gyaran motar.

Sai dai wata majiya ta daban ta ce sojojin sun bar motar ne bayan ta lalace sannan suka fara tafiya da kafa zuwa sansaninsu tare da taimakon wani farar hula da ya san yankin.

Kara karanta wannan

FBI ta gano yadda matasa suka hadu, aka kitsa mummunan hari kan masallaci a Amurka

A cewar majiyar, maharan sun kai wa tawagar hari ne yayin da suke hanyar komawa Illela, tana mai cewa:

“An kashe sojoji bakwai tare da farar hular da ke taimaka musu."
An ce Lakura sun rutsa sojoji ne lokacin da motarsu ta lalace a Sokoto.
Taswirar jihar Sokoto, inda aka ce Lakurawa sun kashe sojoji 7. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kai gawarwakin Sokoto

Mazauna yankin sun bayyana cewa an fara gano gawarwaki shida a wurin harin kafin daga bisani aka sake gano gawar wani soja a cikin daji washegari.

Wani mazaunin yankin ya ce an kirga gawarwaki bakwai gaba daya bayan gano gawar wani soja da aka rasa, a cewar rahoton jaridar Punch.

Wani jami’in gwamnati a yankin ya kuma bayyana cewa daya daga cikin wadanda aka kashe babban jami’in soja ne mai mukamin Laftanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com