Da Gaske Gwamnoni 22 Sun Goyi bayan Takarar Jonathan? An Gano Kuskuren Ndume
Abuja - A ranar 8 ga Yuni, Ali Ndume, Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, ya yi iƙirarin cewa gwamnoni 22 da aka zaɓa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP sun goyi bayan Shugaba Goodluck Jonathan a lokacin zaɓen 2015.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Da yake magana a wata hira da aka yi da shi Sanata Ali Ndume ya ce duk da goyon bayan gwamnonin, Goodluck Jonathan ya faɗi zaɓen tazarcensa na 2015 “cikin kunya”.

Asali: Twitter
'Gwamnoni 22 sun goyi bayan Jonathan' - Ndume
Yayin zantawa da Channels TV, sanatan na Borno ya yi gargadi Shugaba Bola Tinubu da kada ya bari goyon bayan gwamnoni ya rude shi, domin gudun sake maimaita abin da ya faru a 2015.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Jonathan yana da goyon bayan gwamnoni 22 a lokacin zaben 2015, kamar yadda Tinubu ya samu yanzu. Amme ya faru? Jonathan ya faɗi zaɓe cikin kunya a lokacin."
- Sanata Ali Ndume.
A watan Mayun 2025, muka ruwaito cewa gwamnonin APC sun amince da Tinubu a matsayin ɗan takara ɗaya tilo na jam'iyyar APC da zai fafata a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Yadda PDP ta samu rabuwar kawuna a 2011-2015
A ƙarshen zaɓen 2011, PDP tana da iko a matakin tarayya bayan Jonathan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Jam'iyyar tana da ikon aƙalla jihohi 22, yayin da jam'iyyar ACN ke mulki a jihohi biyar na Kudu maso Yamma da Edo; ANPP kuma tana da iko a jihohi uku yayin da APGA, LP, da CPC ke da iko da aƙalla jiha ɗaya.
Jonathan, wanda shi ne mataimakin shugaban ƙasa ga tsohon Shugaba Umaru Musa Yar’Adua, ya zama shugaban ƙasa lokacin da Yar’Adua ya rasu a watan Mayu 2010.
Idan za a tuna, ya kammala wa'adin marigayi Yar’Adua kuma ya lashe zaɓen 2011.
Rarrabuwar kawuna a PDP ta fara ne lokacin da wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar suka nace cewa Jonathan, ɗan Kudu, ya bar ɗan Arewa ya fito takara a 2015 tun da Yar’Adua, ɗan Arewa, bai riga ya kammala wa'adinsa ba ya rasu.
Jonathan ya ki amincewa da wannan bukata, inda ya fito takara a zaben na 2015, sai dai kuma kaddara ta riga fata a kansa, inda hadaddiyar jam'iyyar adawa ta APC ta lashe zaben.
Gwamnoni 7 sun balle daga PDP a 2013
A watan Agusta 2013, tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar da gwamnoni bakwai suka fice daga taron PDP na ƙasa a Eagles Square da ke Abuja.
Gwamnoni bakwan sune: Rabiu Kwankwaso na Kano, Aliyu Wammako na Sokoto, Murtala Nyako na Adamawa, Sule Lamido na Jigawa.
Har il ayau akwai: Muazu Aliyu na Neja, Abdulfattah Ahmed na Kwara, da Rotimi Amaechi na Ribas.
Abubakar Baraje, tsohon shugaban PDP, wasu sanatoji, da mambobin majalisar wakilai suma sun shiga cikin zanga-zangar ficewar daga taron.
Mambobin PDP da suka ji haushi, waɗanda daga baya suka kafa sabuwar PDP (nPDP), sun zargi shugabancin jam'iyyar da Jonathan da cusa ƴan takara da kuma kin bin dokar jam'iyyar.
A watan Nuwamba 2013, nPDP – ɓangaren da ya balle – ya shiga sabuwar APC da aka kafa.
Daga cikin gwamnonin PDP bakwai da suka shiga zanga-zangar ficewar, biyar daga cikinsu sun shiga APC, ban da Sule Lamido da Muazu Aliyu. Sakamakon haka, adadin gwamnonin PDP ya ragu kafin zaɓen 2015.
Buhari ya kayar da Jonathan a 2015
A ranar 1 ga Afrilu, 2015, aka bayyana tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya yi takara karkashin APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2015.
Buhari ya samu jimillar kuri'u 15,424,921 inda ya kayar da Jonathan na PDP, wanda ya samu kuri'u 12,853,162 a zaɓen.
Zaɓen ya nuna zuwan ƙarshen mulkin PDP na tsawon karni kusan karni daya da rabi, tun lokacin da jam'iyyar ta karbi mulki a lokacin da ƙasar ta dawo mulkin dimokuraɗiyya a 1999.

Asali: Facebook
Gwamnonin PDP 22 sun goyi bayan Jonathan a 2015?
A watan Satumba 2014, gwamnonin PDP suka goyi bayan Jonathan a matsayin ɗan takara tilo na jam'iyyar gabanin babban zaɓen 2015.
Gwamnonin da suka halarci taron sune Godswill Akpabio na Akwa Ibom, Idris Wada na Kogi, Liyel Imoke na Cross Rivers da Ramalan Yero na Kaduna.
Sauran gwamnonin sun hada da; Theodore Orji na Abia, Emmanuel Uduaghan na Delta, Jonah Jang na Filato, Seriake Dickson na Bayelsa da Sullivan Chime na Enugu.
Har ila yau, daga cikin gwamnonin, akwai Gabriel Suswam na Benuwai, Umaru Fintiri na Adamawa (a matsayin mai rikon kwarya), da Garba Umar na Taraba.
Gwamnonin Jigawa, Katsina, Sokoto, da Kebbi ba su samu damar halartar taron ba, amma sun tura mataimakansu su wakilce su.
Gwamnonin PDP 16 ciki har da mataimakan gwamnoni sun halarci taron da aka goyi bayan Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa tilo na jam'iyyar.
An tabbatar da cewa ba gwamnoni 22 ne suka goyi bayan Jonathan ba, saboda biyar daga cikinsu sun riga da sun sauya sheka zuwa sabuwar APC da aka kafa a lokacin.
Iƙirarin da Sanata Ali Ndume ya yi na cewa gwamnoni 22 sun goyi bayan Jonathan don zaɓen 2015 ba daidai bane, kamar yadda rahoton The Cable ya nuna.
Duk da haka dai, tsohon shugaban kasar ya samu goyon bayan gwamnoni da-dama na PDP da ba su iya hana APC ta doke jam'iyyarsu a 2015 ba.
Ndume ya ki marawa Tinubu baya kan tazarce
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa baya goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ya sake tsayawa takara a babban zaɓen 2027.
Ya bayyana hakan ne bayan matsayar gwamnonin APC 22 na nuna goyon bayansu ga Shugaba Tinubu a matsayin ɗan takararsu a zaɓe mai zuwa.
A cewar Ndume, halin da ƙasar ke ciki a yanzu ya nuna cewa jama'a suna cikin matsanancin hali, don haka, ya ce bai dace a riƙa maganar sake takarar Tinubu ba a halin yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng