Matakin da Isra’ila Ta Dauka kan Sojan da Ya Ruguza Mutum Mutumin Yesu
- Rundunar tsaron Isra'ila ta dauki mummunan mataki kan wani soja da ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ruguza mutum-mutumin Yesu
- Sojoji sun hukunta sojojin biyu da tsare su na kwanaki 30 bayan lalata mutum-mutumin Yesu wanda dayan ya dauka a waya a Lebanon
- Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nuna takaici kan lamarin, yayin da mutane a yankin suka yi Allah-wadai da abin da ya faru
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Rundunar sojin Isra’ila ta dauki mataki kan wani soja da ya jawo maganganu a duniya kan ruguza mutum-mutumin Yesu.
Rundunar ta ce za ta tsare wasu sojoji biyu na tsawon kwanaki 30 bayan sun lalata mutum-mutumin Yesu a kudancin Lebanon.

Source: Twitter
Laifuffukan da ake zargin sojan da aikatawa
A cewar rundunar, an kuma cire sojojin daga aikin yaƙi bayan bincike ya nuna cewa abin da suka aikata ya saɓa da dokoki da ƙa’idojin rundunar, cewar BBC.

Kara karanta wannan
Za a kai wadanda suka shirya yi wa Tinubu juyin mulki kotu, an jero laifuffukansu
Haka kuma, wasu sojoji shida da suka halarci wurin amma suka kasa tsoma baki ko bayar da rahoto za a hukunta su saboda zargin ko in kula da kuma barin barna a bainar jama'a.
Lamarin da ya faru a kauyen Debel ya jawo suka daga sassa daban-daban na duniya bayan hoton abin da ya faru ya bazu sosai a kafafen sada zumunta.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa abin ya girgiza shi kuma ya nuna takaicinsa kan abin da ya faru.
Rundunar sojin ta ce ta maye gurbin mutum-mutumin da aka lalata tare da haɗin gwiwa da al’ummar yankin cikin gaggawa.
Ta kuma jaddada cewa ayyukanta a Lebanon suna nufin yaƙi da ƙungiyoyin da take kira ‘yan ta’adda kamar Hezbollah, ba fararen hula ba.

Source: Facebook
Shugaban coci ya yi Allah-wadai da lamarin
Shugaban cocin yankin, Father Fadi Flaifel, ya yi Allah-wadai da abin, yana mai cewa hakan cin zarafi ne ga addini da kuma haƙƙin ɗan Adam.
Jakadan Amurka a Isra’ila, Mike Huckabee, ya buƙaci a ɗauki mataki mai tsauri da gaggawa kan lamarin.
Wannan na zuwa ne yayin da dubban sojojin Isra’ila ke ci gaba da kasancewa a Kudancin Lebanon bayan tsagaita wuta da aka cimma, cewar New York Times.
Rikicin tsakanin Isra’ila da Hezbollah ya haifar da asarar rayuka da dama da kuma gudun hijira ga mutane sama da miliyan guda a yankin.
Iran/Isra'ila: Farashin kororon roba zai tashi
A wani labarin, an ji cewa ana fargabar farashin kwaroron roba na duniya na iya tashi sosai bayan rikicin Iran ya haddasa tangarda a hanyoyin samar da kayayyaki.
Kamfanin Karex ya bayyana cewa zai kara farashi da kaso 20 zuwa 30 saboda karin kudin jigila da jinkirin kaya da ke haddasa karancin kaya.
Masana sun gargadi cewa ci gaba da wannan matsala zai iya jawo karanci musamman a kasashe masu karamin karfi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
