Sanata Ndume Ya Ƙi Marawa Tinubu baya kan Batun Tazarce, Ya Fadi Dalilansa
- Sanata Ali Ndume ya nesanta kansa daga goyon bayan Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sake tsayawa takara a babban zaben 2027
- Ya bayyana haka ne bayan matsayar gwamnonin APC 22 na goyon bayan Shugaba Tinubu a matsayin dan takararsu a zabe mai zuwa
- Ndume ya ce halin da kasa ke ciki a yanzu, jama'a suna cikin mawuyacin halin da bai dace a rika maganar sake takarar Tinubu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, Ali Ndume, ya ce baya goyon bayan kudurin gwamnonin APC 22 dake son Bola Tinubu ya sake tsayawa takara.
A cewarsa, duk da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya samu goyon bayan gwamnonin PDP 22 a zaben 2015, hakan bai hana ya fadi zaben ba a wancan lokaci.

Asali: Facebook
Sanata Ndume, wanda ya kwashe sama da shekaru 20 a Majalisar Tarayya, ya bayyana hakan ne a shirin Sunday Politics na Channels Television.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ndume ya barranta daga goyon bayan Tinubu
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa a ranar 22 ga Mayu, 2025, gwamnonin APC 22 sun amince da Tinubu a matsayin dan takarar jam’iyyar a 2027.
Duk da kasancewarsa babban jigo a APC, Ndume ya ce bai goyi bayan wannan mataki ba, yana mai cewa halin da ake ciki a ƙasar yanzu yana da matuƙar muni.
Ya koka kan halin tsananin rayuwa, hauhawar farashin kayayyaki da kuma tabarbarewar tsaro da ke addabar sassan Najeriya.
Sanata Ndume ya fice daga taron goyon bayan Tinubu
Ndume ya bayyana cewa ya bar Banquet Hall na fadar shugaban kasa a Abuja lokacin da aka fara batun goyon bayan shugaban kasa domin tazarce.
Ya ce:
“Na halarci wurin amma ba wannan ne dalilin zuwa na ba; na je taron koli ne. Da na fahimci cewa ba taron koli ba ne, sai kawai aka saka kuri’ar murya don nuna goyon bayan Shugaba Tinubu, na fice.
Amma hakan ba yana nufin ni ba dan jam’iyya ba ne. Yawancin mutane sun yarda da batun, amma kadan daga cikinmu mun ga ba daidai ba ne.”

Asali: Twitter
Ya kara da cewa:
“An taba yin haka a baya – ba sau daya ba, ba sau biyu ba. An taba yin hakan lokacin Jonathan, kuma hakan bai canza komai ba." “Ina fata shugaban zai kalli tarihi, ya fahimci cewa taron mutane don goyon bayanka ba yana nufin komai ba ne.”
Ali Ndume ya yabawa Bola Tinubu
A baya, kun samu labarin cewa Ali Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya dan tsahirta da sukar Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Sanata Ndume ya zazzagawa Tinubu ruwan yabo kan matakin da ya dauka na hana shigo da kayayyakin da za a iya samarwa a cikin gida don bunkasa kasuwanci.
A cewarsa, wannan mataki zai taimaka sosai wajen bunkasa masana’antu, samar da ayyukan yi ga matasa, da karfafa darajar Naira domin rage fitar da kudaden waje.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng