Gwamnonin APC Sun Yi Matsaya kan Takarar Tinubu a Zaben 2027
- Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya sun gamsu da kamun ludayin shugabancin mai girma Bola Tinubu
- Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodimma ya gabatar da ƙudiri domin a amince Bola Tinubu ya zama ɗan takara a 2027
- Ƙudirin nasa ya samu amincewar dukkanin mahalarta taron ƙoli na jam'iyyar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC ta amince da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Ƙungiyar gwamnonin ta amince da Bola Tinubu a matsayin ɗan takara ɗaya tilo na jam’iyyar domin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta ce gwamnan jihar Imo kuma shugaban ƙungiyar, Hope Uzodimma, ne ya sanar da wannan matsaya a taron koli na jam’iyyar APC da ake gudanarwa a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin APC sun amince da tazarcen Tinubu
Yayin da yake jawabi a wajen taron Gwamna Hope Uzodimma, ya bayyana cewa gwamnonin jam’iyyar sun amince da Shugaba Tinubu a matsayin ɗan takara guda ɗaya na APC a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Gwamna Uzodimma ya gabatar da ƙudirin goyon bayan sake tsayawa takarar Tinubu, kuma gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya marawa ƙudirin baya, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Bayan haka, Gwamna Uzodimma ya tambayi taron ko an amince da ƙudirin, kuma dukan mahalarta taron suka amince da shi da murya ɗaya.
A madadin gwamnonin jam’iyyar APC, Uzodimma ya bayyana cewa sun haɗa kai wajen goyon bayan yunƙurin Shugaba Tinubu na neman wa’adi na biyu.
Meyasa gwamnonin APC suka goyi bayan Tinubu
"Domin Najeriya ta samu ci gaba cikin sauri, dole ne a sake amfani da shugaban da muke da shi yanzu kuma a ɗauke shi a matsayin ɗan takarar mu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.”
“Haka kuma, an umurci dukkan gwamnonin da jam’iyyar APC ta samar da su, da su ɗauki nauyin tallata manufofin gwamnatin tarayya a jihohinsu, su mamaye siyasar yankunansu, tare da tabbatar da nasarar jam’iyyar a dukkan zaɓukan da za a gudanar a shekarar 2027."
“Saboda haka, cikin tawali’u da godiya ga Allah Madaukaki, na gabatar da wannan ƙudirin cewa wannan babban taro ya amince da matsayar gwamnonin jam’iyyar cewa shugaban ƙasa Tinubu ya zama ɗan takarar mu a 2027, sannan gwamnonin su ɗauki nauyin cika wannan alƙawari. Wannan ne ƙudirina."
- Gwamna Hope Uzodimma

Asali: Twitter
Duk da cewa Tinubu yana tsakiyar wa’adin mulkinsa na farko, tattaunawa kan neman wa’adi na biyu sun fara mamaye harkokin siyasar Najeriya.
Har yanzu dai Shugaba Tinubu bai nuna aniyar sake neman takarar shugaban ƙasa ba a zaɓen 2027.
Peter Obi ya musanta ganawa da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya musanta neman ganawa da Bola Tinubu a birnin Rome.
Peter Obi ya bayyana cewa rahoton da ke cewa ya nemi ganawa da Tinubu kan bashin da ake bin bankin Fidelity, babu ƙamshin gaskiya a cikinsa.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya nuna cewa masu yaɗa jita-jitar suna yi ne kawai domin ganin sun ɓata masa suna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng