2027: APC Ta Yi Barazanar Hukunta Ndume kan Maganar Faduwar Tinubu Zabe

2027: APC Ta Yi Barazanar Hukunta Ndume kan Maganar Faduwar Tinubu Zabe

  • Jam’iyyar APC ta gargadi Sanata Ali Ndume kan kalamansa da ya danganta Bola Tinubu da abin da ya faru da Goodluck Jonathan a 2015
  • APC ta bayyana cewa tana yarda da bambancin ra’ayi, amma tana da hanyoyi na ladabtar da ‘ya’yanta da ke aikata ba daidai ba
  • Sanata Ndume ya nuna damuwarsa cewa matsin rayuwa da goyon bayan bogi na iya janyo wa Tinubu rashin nasara a zaben 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta yi tir da furucin da Sanata Ali Ndume ya yi inda ya kwatanta halin da Bola Tinubu ke ciki da na Goodluck Jonathan kafin zaben 2015.

Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu ya bayyana damuwarsa a wata tattaunawa, inda ya ce akwai yiwuwar Tinubu zai gamu da abin da Jonathan ya fuskanta idan bai dauki darasi ba.

APC ta gargadi Ndume kan sukar Tinubu
APC ta gargadi Ndume kan kwatanta Tinubu da Jonathan. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa jam’iyyar APC ta ce tana maraba da ra’ayoyi daban-daban daga mambobinta, amma sai dai dole ne ra’ayoyin su kasance cikin doka da tsarin jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman Ndume da suka janyo ce-ce-ku-ce

A yayin tattaunawa da Channels TV, Sanata Ndume ya ce goyon bayan da wasu ‘yan jam’iyyar ke yi wa Shugaba Tinubu ba ya nuna tabbacin kan kawo sauyi a kasa.

Ya ce:

“Shugaba Tinubu na iya fuskantar irin abin da Jonathan ya fuskanta.
"Jonathan yana da gwamnonin jihohi 22 da suka mara masa baya, amma hakan bai hana shi faduwa ba. Irin wannan na iya maimaituwa.”

Ndume: APC ta yi martani da gargadi

A martanin da jam’iyyar ta fitar ta bakin daraktan yada labarai na kasa, Bala Ibrahim, ta ce Sanata Ndume na da matsayi mai girma a jam’iyyar.

Sai dai duk da haka, APC ta ce hakan ba ya nufin yana da ‘yancin furta duk wani abu da zai karya tsarin da aka shimfida.

Bala Ibrahim ya ce:

“Sanata Ndume mutum ne da jam’iyya ke mutuntawa.
"Amma dole ne a fahimci cewa duk ra’ayin da ba ya girmama tsarin jam’iyya ko kuma ya zama abin ci gaba, ba za a lamunce masa ba.”

Bala Ibrahim ya kara da cewa APC jam’iyya ce da ke karɓar ra’ayoyi masu tasiri, amma ba ta yarda da cin zarafi ko kalaman da ka iya raunana jam’iyya ko kasa ba.

Ya ce:

“Idan aka samu mambobi da suka saba wa ka’idoji, akwai tsari a cikin jam’iyya da ke kula da ladabtarwa.
"Wannan tsarin ya wuce ikon darakta kawai, kuma ana amfani da shi idan bukata ta taso.”
APC ta ce za ta hukunta masu laifi
APC ta ce tana da tsarin hukunta masu laifi bayan kalaman Ndume. Hoto: Getty Images
Asali: Twitter

PDP ta zargi Tinubu da kawo wahala Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta ce gwamnatin Bola Tinubu da APC sun jefa 'yan Najeriya cikin wahala.

PDP ta yi magana ne yayin sakon barka da sallah da ta fitar tana mai cewa an kara samun wahalhalun rayuwa a Najeriya.

A saboda haka ne jam'iyyar PDP ta bukaci gwamnatin Bola Tinubu da ta rage kudin man fetur da lantarki domin rage radadin rayuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng