Muna nan daram a APC – Mambobin sabuwar PDP (nPDP)

Muna nan daram a APC – Mambobin sabuwar PDP (nPDP)

Alhaji Kawu Baraje, shugaban mambobin jam’iyyar PDP da suka canja sheka zuwa APC kafin zaben 2015, y ace ba zasu fice daga jam’iyyar APC ba kamar yadda rahotanni ke bayyanawa ba.

Ya bayyana haka ne yau, Litinin, ga manema labarai jim kadan bayan fitowa daga wata ganawa da kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC a Abuja.

Baraje da ragowar ‘yan jam’iyyar PDP dake cikin APC sun mika wata takardar korafi ga shugabancin jam’iyyar APC inda suka bayar da kwanaki 7 a dauki mataki a kan korafe-korafen da suka lissafa.

Muna nan daram a APC – Mambobin sabuwar PDP (nPDP)
Alhaji Kawu Baraje

‘Yan kungiyar nPDP sun zargi gwamnati da shugabancin jam’iyyar APC da jingine su gefe guda tare da kin damawa da su a harkokin gwamnati da na jam’iyya.

Baraje ya bayyana cewar sun fara saito tad a shugabancin jam’iyyar APC tare da bayyana shugabannin APC da cewar masu kunnuwan sauraro ne.

DUBA WANNAN: Mamba a majalisar Wakilai ya bankado cushe a kasafin kudin bana

“Mu ‘yan jam’iyyar APC ne, ofishin APC ofishin mu ne. Mun roki jam’iyyar APC ta tsayar mana day au a matsayin ranar da zamu gana, kuma sun yi hakan. Ganawar ta mu tayi armashi matuka. Mun fara tattaunawa kuma zamu cigaba domin maganganu ban a rana daya bane,” in ji Baraje.

Da yake nasa jawabin a madadin shugabancin jam’iyyar APC na kasa, mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Shu’aibu Lawal, y ace, “bamu gama tattaunawa ba, sun rubuto mana takarda kuma bamu dauki korafen-korafen su da wasa ba saboda ‘yan jam’iyyar APC ne su ma.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng