An Gano 'Yan Najeriya 10 da Suka Yi Mu'amala da Ɗan China Mai Ɗauke da Korona

An Gano 'Yan Najeriya 10 da Suka Yi Mu'amala da Ɗan China Mai Ɗauke da Korona

  • Gwamnatin Jihar Cross River ta gano tare da killace mutane 10 da suka yi mu’amala da wani ɗan ƙasar China da ya dawo dauke da cutar COVID-19
  • Babban jami’in binciken cututtuka na jihar, Dr. Inyang Ekpenyong, ya ce an gano mutanen ne ta hanyar binciken waɗanda suka yi mu’amala da majinyacin
  • Hukumar lafiya ta tabbatar da cewa ɗan Chinan na karɓar magani a asibitin koyarwa na UCTH, sannan ta yi kira ga jama’a da su koma amfani da takunkumi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Cross River – Gwamnatin Jihar Cross River ta sanar da killace mutane 10 waɗanda aka tabbatar sun yi mu’amala da wani ɗan ƙasar China wanda ya dawo da cutar COVID-19 Najeriya.

Wannan sanarwa na zuwa ne kwanaki biyu bayan bayyanar rahoton bullar cutar a jihar.

Kara karanta wannan

'Ƙarfi ya ci,' Iran ta yi abin mamaki da jiragen dakon mai 3 suka shiga Hormuz

An sake samun bullar COVID 19 a jihar Cross Rivers
Ma'aikatan lafiya na gudanar da gwajin COVID-19 a jihar Legas. Hoto: Emmanuel Osodi/Majority World/Universal Images Group via Getty Image
Source: Getty Images

An killace mutum 10 kan COVIS-19

Dokta Inyang Ekpenyong, babban jami’in binciken cututtuka na jihar, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa hukumarsa ta ziyarci wurin aikin ɗan ƙasar Chinan da ke ƙaramar hukumar Akamkpa domin gudanar da bincike na musamman.

A cewar Dokta Ekpenyong, an umarci mutanen 10 da su zauna a gidajensu ba tare da fita ba, domin kiyaye yaɗuwar cutar zuwa ga sauran jama'a.

Ta ƙara da cewa:

"Mun taƙaita zirga-zirgar mutanen zuwa gidajensu kawai, domin tabbatar da cewa ba su yaɗa alamun cutar ga wasu ba. Shi kuwa ɗan ƙasar Chinan, yana samun sauƙi sosai a asibitin koyarwa na UCTH."

Har yanzu ba a kawar da Korona ba

Jami'ar ta tunatar da jama'a cewa cutar COVID-19, wadda ta ɓalle kimanin shekaru shida da suka gabata, har yanzu ba a gama kawar da ita gaba ɗaya daga duniya ba.

Ta yi kira ga mutane da su koma al'adar wanke hannu, amfani da sinadarin tsaftace hannu, da kuma sanya takunkumin hanci, in ji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

An yi kira ga 'yan Cross River da su kwantar da hankula bayan bullar Covid-19 a jihar.
Wasu allurori na rigakafin annobar Covid-19. Hoto: Getty Images
Source: UGC

"Babu dalilin firgita" — Kwamishinan Lafiya

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Henry Egbe Ayuk, wanda shi ne ya fara bayyana labarin dawowar cutar a ranar Litinin, ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnati ta riga ta shirya tsaf domin dakile yaɗuwar cutar.

Dakta Ayuk ya bayyana cewa ko da yake duniya na fuskantar barazanar sake bullar cutar saboda zirga-zirgar mutane daga ƙasa zuwa ƙasa, amma jihar Cross River ta kunna dukkan matakan kariya na lafiyar al'umma.

"Cutar COVID-19 ba a Najeriya kaɗai take ba, amma muna da kyakkyawan shiri na dakile ta. Babu buƙatar tada hankali."

- Dakta Henry Egbe Ayuk.

Dan China ya shigo Najeriya da Covid-19

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnati ta tabbatar da bullar cutar Covid-19, inda wani dan kasar China ya kamu da cutar wanda ya daga hankulan al'umma.

Sanarwar gwamnati ta tabbatar da cewa hakan ya faru ne bayan ɗan China ya dawo Najeriya daga kasarsa ta haihuwa.

Kwamishinan lafiya a Cross River, Dakta Henry Ayuk, ya ce an gano cutar bayan an dauki samfurin majiyyacin a asibitin koyarwa na Calabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com