Murna Ta Koma Ciki: Gwamnatin Tinubu Ta Gargaɗi Gwamnoni, Masu Sauya Sheƙa zuwa APC
- Gwamnatin Tarayya ta ce sauya sheka zuwa APC ba zai hana gurfanar da gwamnonin da ake zargi da cin hanci ba
- Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi ya ce zargin haduwa da gwamnonin jihohin kafin sauya sheka karya ce tsagwaronta
- EFCC ta ce shugabanta ba shi da alaka da siyasa, kuma ba a yi wani taro da gwamna kafin sauya sheka zuwa APC ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya a ranar Juma’a ta yi gargadi ga masu sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
Gwamnatin ta yi gargadin ne ga masu laifuffuka da EFCC ke tuhuma inda ta ce hakan ba zai hana gurfanar da masu laifi ba.

Asali: Facebook
Gwamnatin Tinubu ta gargadi masu sauya sheka
Ministan Shari’a kuma Attoni-Janar na Tarayya, Prince Lateef Fagbemi, SAN, ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce gwamnatin Bola Tinubu za ta ci gaba da mutunta doka kuma ba za ta ja da baya wajen yaki da cin hanci da rashawa ba.
Fagbemi ya bayyana matsayar gwamnatin Tinubu ne yayin da yake karyata ikirarin wani hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Ya ce babu gaskiya cikin zargin da Paul Ibe ya yi cewa EFCC da babban lauya sun gana da gwamnoni kafin su sauya sheka.
Fagbemi ya ƙaryata ganawa da wasu gwamnoni
Har ila yau, Lateef Fagbemi ya kira wannan zargi da cin zarafi, yana mai cewa kodayake Ibe bai fadi sunan gwamnonin ba, mutane na iya fahimtar wadanda ake nufi.
Ya ce:
“Muna so mu bayyana karara cewa wannan zargi karya ne, tunanin Paul Ibe kawai ne, muna da tabbaci cewa shugaban EFCC ba su gana da kowanne gwamna ba kamar yadda aka zarga.
“Muna rokon jama’a da su yi watsi da wannan batu saboda yunƙurin bata sunan gwamnatin Bola Tinubu ne kawai.
“Gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da mutunta doka kuma ba za ta dakata da yaki da rashawa ko da kuwa ta taba kowa ba."

Asali: Facebook
Martanin EFCC kan zarge-zargen da ake yi
EFCC ma ta fitar da wata sanarwa daga mai magana da yawunta, Mr. Dele Oyewale da aka wallafa a Facebook, tana karyata zargin da Ibe ya yi.
Hukumar ta ce hadimin Atiku ya bayyana ra’ayinsa ne kan siyasar hamayya da sauya sheka a hira da ya yi ranar 22 ga Mayu.
“Olukoyede ya sha nanatawa cewa ba shi da ra’ayin siyasa, EFCC kuma tana aiki da tsantsar gaskiya ba tare da son rai ba.
“Jama’a su yi watsi da zargin haduwa da gwamna, domin wannan magana karya ce da Ibe ya kirkira."
- Cewar sanarwar
Tinubu ya ji dadin sauya sheka zuwa APC
Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi magana game da sauyin sheka da ke faruwa a cikin APC.
Shugaban ya ce yana kuma fatan karin ‘yan adawa za su bi sahu inda ya kare kansa daga suka cewa zai mayar da Najeriya mulkin jam'iyya daya.
A taron APC, shugabannin jam’iyya sun amince da Tinubu a matsayin dan takara tilo na shekarar 2027 da ke tafe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng