"Arewa ba Ta Adawa da Tinubu," Tsohon Minista Ya Yi Magana kan 2027
- Tsohon Minista, Muktar Shagari ya bayyana cewa ‘yan Arewa ba su da rashin jituwa da Shugaba Bola Tinubu, kuma za su ba shi goyon baya a 2027
- Ya bayyana cewa APC ta bayyana shugaba Tinubu a matsayin dan takararta saboda a kwantar masa da hankali ya ci gaba da mulki yadda ya kamata
- Shagari ya ce ana ganin ci gaba musamman a jihohin Arewa maso Yamma kamar Sakkwato, inda ake samun ci gaba sosai a harkar tsaro
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Ministan Harkokin Ruwa, Muktar Shagari, ya bayyana cewa babu wata gaba ko rashin jituwa a tsakanin ‘yan Arewa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
A cewarsa, 'ya'yan jam’iyyar APC mai mulki suna da yakinin cewa shugaban kasa na da kwarewar da zai gyara Najeriya, musamman idan ya samu wa'adi na biyu.

Asali: Facebook
A wata hira da ya yi da Arise News a ranar Juma’a, Shagari ya ce dole ne a sake zaben Tinubu domin ya kammala aiwatar da manufofinsa da ya fara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shagari ya magantu kan sake zaben Tinubu
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Shagari ya ce an bayyana Bola Ahmed Tinubu ne ya fi dacewa da ci gaban da mulkin Najeriya.
Ya ce:
“Domin Shugaba Tinubu ya aiwatar da shirye-shiryensa da ya yiwa ’yan Najeriya alkawari, yana bukatar wa’adi na biyu, kuma mu a jam’iyyar APC muna da yakini zai yi abin arziki.
"Abin da ya kamata mu yi shi ne mu ba shi goyon baya ta fuskar siyasa da, kuma mu tabbatar cewa babu wanda zai hana shi natsuwa ta hanyar tsayawa takara da shi.”
Dalilin bayyana Tinubu a matsayin dan takara
Tsohon ministan ya ce jam’iyyar APC ta bayyana Tinubu a matsayin dan takararta daya tilo a 2027 ne domin kauce wa ruɗani da zai hana shugaban kasa natsuwa a aikin mulki.

Asali: Facebook
A cewarsa:
“Shugaban kasa yana kokari matuka wajen ganin ya gyara kasar nan, kuma yanzu ana fara ganin sakamakon hakan, kasar na cigaba sosai."
Shagari ya bayyana cewa ya na da tabbacin yankin Arewa zai ba Shugaba Tinubu cikakken goyon bayan da yake bukata domin lashe zaben 2027.
Ya ce ta haka ne za a samu tabbatar da ci gaba mai dorewa a Najeriya, musamman wajen ci gaba da ayyukan Bola Tinubu.
An fara nazarin kifar da gwamnatin APC
A wani labarin, mun wallafa cewa hadakar ’yan adawa ta dora wa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan Kuros Riba, Liyel Imoke, alhakin nemo masu mafita.
An nada Amaechi da Imoke ne domin su duba yiwuwar kafa sabuwar jam’iyya ko kuma su hada kai da wata jam’iyya da ke akwai a halin yanzu, domin fuskantar jam’iyyar APC.
Imoke na jagorantar kwamitin da ke duba yiwuwar hadewa da wata jam’iyya yayin da Rotimi Amaechi ke jagorantar wani kwamitin daban da ke duba yiwuwar kafa sabuwar jam’iyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng