2027: Tinubu Ya Tura Saƙo ga Jagororin APC yayin da Ake Shirin Haɗaka Mai Ƙarfi

2027: Tinubu Ya Tura Saƙo ga Jagororin APC yayin da Ake Shirin Haɗaka Mai Ƙarfi

  • Bola Ahmed Tinubu ya ce yana maraba da sauyin sheka da ke faruwa da cikin APC, yana kuma fatan karin ‘yan adawa za su bi sahu
  • Ya kare kansa daga suka, yana cewa “ba za ka zargi mutum da tserewa jirgin da ke nitsewa ba”, yana mai cewa siyasa ce kawai
  • A taron APC, shugabannin jam’iyya sun amince da Mai girma Tinubu a matsayin dan takara daya tilo na shekarar 2027 da ke tafe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan siyasar Najeriya gabannin zaben 2027.

Bola Tinubu ya ce yana maraba da sauyin sheka da ke faruwa a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya a yanzu.

Tinubu ya magantu kan masu sauya sheƙa
Tinubu ya bukaci jagororin APC su ci gaba da kokari. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tinubu ya yaba da sauya sheka zuwa APC

Shugaban ya bayyana hakan ne a taron kasa na APC da aka gudanar ranar Alhamis a birnin Abuja, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya bayyana cewa yana sa ran karin 'yan adawa za su biyo baya duba da irin kimar APC ke da shi a Najeriya.

Shugaban ya jaddada matsayinsa na maraba da masu sauya sheka da kuma kore zargin mayar da kasar ta jam'iyya daya.

A cikin jawabinsa, Bola Tinubu ya ce yana farin ciki da yadda 'yan siyasa ke sauya sheka zuwa APC, kuma ya bukaci shugabannin jam’iyyar da su kara gayyatar wasu.

Tinubu ya bukaci nakasa jam'iyyun adawa
Tinubu ya nuna jin dadi kan sauya sheka zuwa APC. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Facebook

Sauya sheka: Bola Tinubu ya soki masu suka

Shugaba Tinubu ya soki masu sukar gwamnati da zargin cewa APC na kokarin kafa jam’iyya daya tilo, yana mai cewa hakan bai sabawa doka ba.

Ya ce:

“Ba za ka zargi mutum da tserewa daga jirgin da ke nitsewa ba, musamman idan ba shi da rigar ruwa domin ceton rai. Ina farin ciki.

“Ina farin ciki da abin da ke faruwa, kuma ina sa ran karin mutane za su zo. Wannan ita ce siyasa. Wannan mulkin dimokuradiyya ne.
“Mu sani cewa ‘yancin shiga kowace jam’iyya ba laifi ba ne, muna maraba da ku zuwa wajen masu kishin kasa, ku share su tsaf!”

Ganduje ya marawa Tinubu baya a 2027

Tun da farko, shugabannin kwamitin gudanarwa na APC sun marawa Tinubu baya kan zaben 2027, cewar rahoton Punch.

Kwamitin karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana goyon bayansu ga Tinubu a matsayin dan takara na 2027.

Ganduje ya yaba da salon mulkin Tinubu da irin abubuwan ci gaba da ya kawo wanda ya cancanci sake zama ɗan takara tilo na jam'iyyar a zaben 2027 da ke tafe.

2027: Gwamnonin APC sun marawa Tinubu baya

A baya, mun ba ku labarin cewa gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya sun gamsu da kamun ludayin shugabancin Bola Tinubu.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodima shi ya tabbatar da haka domin a amincewa da Tinubu ya zama ɗan takara a 2027.

Hakan ya samu amincewar dukkanin mahalarta taron ƙoli na jam'iyyar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa domin ba Tinubu goyon baya mai ɗorewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.