An Zo wajen: Tinubu Ya Yi Magana kan Shirin Maida Najeriya karkashin Jam'iyya 1

An Zo wajen: Tinubu Ya Yi Magana kan Shirin Maida Najeriya karkashin Jam'iyya 1

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan zargin da ake yi na APC na shirin maida Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya
  • Mai girma Bola Tinubu ya nuna cewa bai kamata a zargi mutane ba saboda sun zaɓi irin mutanen da suke so su yi tarayya da su
  • Ya kuma bayyana cewa jam'iyyar APC za ta ci gaba da yin maraba da duk masu son shigowa cikinta domin ƙofar ta a buɗe take

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa waɗanda ke zargin gwamnatinsa da ƙoƙarin juya Najeriya zuwa ƙarƙashin jam’iyya ɗaya shagube.

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa bai kamata a ga laifin mutane ba saboda irin zaɓin da suka yi na waɗanda suke so su yi tarayya da su.

Shugaba Bola Tinubu
Tinubu ya yi wa 'yan adawa shagube Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron loli na jam’iyyar APC da aka gudana a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis, 22 ga watan Mayun 2025, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya samu goyon baya

A wajen taron dai Shugaba Tinubu ya samu goyon baya daga manyan ƙusoshin jam'iyyar APC.

Gwamnonin APC sun amince da mai girma Tinubu a matsayin ya zama ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Hakazalika shugabannin majalisar tarayya sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da salon mulkin Tinubu, tare da goyon bayan ya yi tazarce.

Tinubu ya yi wa ƴan adawa martani

A wajen Shugaba Tinubu ya gayawa ƴan adawa cewa jam’iyya ɗaya ce kawai ke mulki a Najeriya.

"Ga waɗanda har yanzu ke tunanin tsallake jirginsu, ƙasar nan ta mu ce, ku riƙe ta da kyau. Ga waɗanda ke magana kan tsarin jam’iyya ɗaya, to, jam’iyya ɗaya ce ke mulki kuma ita ce ke jan ragamar burin ƴan Najeriya."

"Ba za ka iya zargin mutanen da suka fice daga jirgi mai nutsewa ba idan ba su da rigar ruwa da za su ceto ransu ba."
"Ina farin ciki da abin da muke da shi, kuma ina sa ran ƙari. Wannan shi ne wasan dimokuraɗiyya. Muna cikin tsarin dimokuraɗiyya na kundin tsarin mulki."

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya ce ba a tilastawa masu shiga APC

Shugaban ƙasan ya ce ba wanda za a tilasta ya zauna inda ba ya so, yana mai jaddada cewa jam’iyyar APC a shirye take ta karɓi ƴan Najeriya da dama da ke da niyyar shigowa cikinta.

Shugaba Bola Tinubu
Tinubu ya ce suna maraba da masu shigowa APC Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter
“Suna tunanin wannan jam’iyyar siyasar ta gaza, amma saboda juriyarku, ba mu taɓa sarewa ba. Mu ne ƴan gaba-gaba. Za mu ci gaba da jajircewa. Ku ci gaba da aiki tuƙuru, ku na ke saurare ba su ba."
“Muna da dama mu sa Afirika ta zama mai ƙarfi, amma ina roƙonku da ku ci gaba da jajircewa. Ga waɗanda ba zan iya ba su mukaman siyasa ba, ku yi haƙuri, za ku yi farin cikin kasancewa cikin wannan jam’iyya."

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya samu goyon baya a Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu jagororin al'umma daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya da Abuja sun nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu.

Jagororin ƙarƙashin ƙungiyar Northern Bridge Builders Forum sun amince Tinubu ya yi tazarce a zaɓen 2027.

Sun bayyana cewa sun cimma wannan matsayar ne saboda kyawawan ayyukan da shugaban ƙasan ya yi a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng