Bayan Barazanar Trump, Amurka Ta kai Hare Hare Kasar Iran

Bayan Barazanar Trump, Amurka Ta kai Hare Hare Kasar Iran

  • Rundunar sojin Amurka ta sanar da cewa ta kai hare-haren Iran bayan harbo jirginta mai saukar ungulu a kusa da mashigar Hormuz
  • Shugaba Donald Trump ne ya ce Iran ta harbo wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojojin Amurka yayin da yake sintiri
  • Tun a ranar Talata Donald Trump ya sha alwashin cewa Amurka za ta mayar da martani ga wannan hari da ya zargi Iran da kai wa kan jirginta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Amurka ta ce ta kammala jerin hare-haren da ta kai wa Iran, yayin da Iran ta mayar da martani ta hanyar harba jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami.

Amurka ta bayyana hare-harenta a matsayin "martani na daidai gwargwado" kan harbo jirgin Apache, yayin da IRGC ta bayyana hare-haren a matsayin “na zalunci.”

Kara karanta wannan

Ana tsaka da yakin Iran da Amurka, Pakistan ta kai mummunan hari a Afghanistan

Shugaba Donald Trump da jiragen yaki
Donald Trump a hagu, jiragen yakin Amurka a dama. Hoto: Getty images
Source: Getty Images

BBC ta rahoto cewa sojojin Amurka sun ce sun kai hari kan tsarin kariyar sararin samaniya, cibiyoyin kula da hare-hare daga ƙasa da kuma wasu wurare.

Sojojin Amurka sun kai hari Iran

Sojojin Amurka a ranar Talata sun kai hare-hare kasr Iran a matsayin martani ga harbo wani jirgin Apache da Trump ya ce Tehran ta yi cikin dare.

Dakarun rundunar Amurka na Centcom sun wallafa a Facebook cewa:

“Mun fara kai hare-haren kare kai kan Iran da ƙarfe 5:00 na yamma a yau bisa umarnin babban kwamandan mu, a martani ga harbo jirgin Apache na rundunar sojin Amurka jiya,”

Centcom ta jaddada cewa aikin:

“Martani ne mai daidai gwargwado ga farmakin Iran da ba shi da wani dalili.”

Jirgin Amurka da aka ce ya fadi

Tun da farko a ranar Talata, sojojin Amurka sun bayyana cewa jirgin AH-64 Apache ya faɗi a yammacin ranar Litinin kusa da gabar tekun Oman yayin da yake sintiri a ruwan yankin.

Kara karanta wannan

Sojojin Iran sun saki bama bamai kan Amurka bayan harin Trump a Tehran

Sun ce an ceto ma’aikatan jirgin biyu ta hanyar amfani da wani jirgin ruwa marar matuƙi na rundunar ruwa cikin sa’o’i biyu, kuma suna cikin yanayi mai kyau.

Donald Trump ya ɗaura alhakin lamarin kan Iran, yana mai cewa dole ne Washington ta mayar da martani ga wannan hari.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump na yi wa Amurkawa jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Mokomar sulhun Iran/Amurka

Amuka da Iran suna ƙara yin musayar hare-haren soji, lamarin da ke jefa yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninsu tun watan Afrilun 2026 cikin shakku.

Wannan sabon hari ya kuma jefa shakku kan ko za a iya sanya hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da Iran cikin kwanaki masu zuwa, kamar yadda Trump ya yi hasashe a wannan makon.

An hana 'yan Iran shiga filin kwallo

A wani labarin, mun kawo muku cewa FIFA ta soke rabon tikitin da aka ware wa magoya bayan Iran domin wasannin rukuni na Kofin Duniya.

Legit Hausa ta rahoto cewa hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar Iran ce ta bayyana hakan a ranar Talata, jim kadan bayan 'yan wasanta sun isa Mexico.

Iran za ta fara wasanta ranar 15 ga Yuni da New Zealand a Inglewood, sai dai kasar ta ce ba za ta iya samar da ko tikiti guda ɗaya ga magoya bayanta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng