2027: Jam'iyyar APC Tana Kwadaitar da Gwamnonin Adawa don Cigaba da Mulki
- Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyya mai mulki ta APC ta fara amfani da wasu dabaru domin jawo yan adawa zuwa cikinta
- An gano cewa jam'iyyar APC na kokarin jawo wasu gwamnonin adawa, daga cikinsu har da Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa
- Daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen jan hankalin gwamnonin akwai alkawarin ba su mukamai ko tikitin tazarce
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Yayin da zaɓen shugaban ƙasa ke ƙara karatowa, tattaunawar haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyu ta ƙara ƙarfi, inda jam’iyyar APC ke kokarin kama gwamnonin adawa.
Wannan ci gaban ya haddasa fargaba wajen mutanen tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi, da kuma jam’iyyun PDP da NNPP.

Asali: Twitter
Majiyoyi sun tabbatarwa da Punch cewa ana yi wa wasu tsofaffin gwamnoni tayin mukaman ministoci, yayin da ake tabbatarwa da gwamnoni masu ci samun tikitin takara karo na biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya gargadi magoya bayan Tinubu
Atiku Abubakar ya yi gargaɗi ga shugabannin jam’iyyun adawa cewa goyon bayan Tinubu domin sake tsayawa takara a 2027 tamkar amincewa da gazawar mulkinsa ne.
Ya bukace su da su goyi bayan ƙoƙarinsa na kafa gamayyar jam’iyyu domin kifar da gwamnatin APC mai mulki.
Mai magana da yawun PDP, Debo Ologunagba, da na NNPP, Ladipo Johnson, sun bayyana cewa 'ya'yansu na fuskantar matsin lamba da amfani da ƙarfin gwamnati don tilasta masu shiga APC.
Martanin jam'iyyar APC ga ’yan adawa
A martani ga zarge-zargen, Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Ajibola Basiru, da Daraktan Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Bala Ibrahim, sun karyata ikirarin.
Sun bayyana cewa ’yan Najeriya na shigowa jam’iyyar APC ne da yardarsu, kuma jam’iyyar na buɗe ƙofofinta domin ƙara yawan 'ya'yansu.
Jam’iyyun PDP, NNPP, da LP na fama da rikice-rikicen cikin gida, lamarin da ya haifar da sauya shekar wasu daga cikin manyansu zuwa APC.
Gwamnonin da jam'iyyar APC ke hari
Akwai gwamnonin da jam'iyya mai mulki ke hari, inda tuni wasu daga cikinsu, kamar Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ke bayyana yiwuwar komawa APC.
Wata majiya kusa da lamarin ta bayyana cewa tsohon gwamnan jihar, Udom Emmanuel, ya shaida wa magoya bayansa cewa Eno ba ya bar PDP a yanzu.

Asali: Facebook
Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo na jam’iyyar APGA, ma ya fito fili ya nuna goyon bayansa ga Tinubu domin sake tsayawa takara.
Rahoton ya kara da cewa Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa yana cikin gwamnoni na adawa da ake ƙoƙarin janyowa su shiga jam’iyyar APC.
A baya, Mashawarcin Shugaban Kasa kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya gana da Gwamna Fintiri na sa’o’i fiye da huɗu a gidan gwamnatin jihar Yola.
Jam'iyyar APC ta goyi bayan Tinubu
A baya, kun ji cewa an gudanar da tattakin nuna goyon baya ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, bayan sauya shekarsa daga NNPP zuwa APC.
Kawu Sumaila, wanda ke wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC tare da dimbin magoya bayansa, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a siyasar Kano.
Kungiyoyi da dama sun halarci taron, ciki har da Waraka Scholars da Waraka TikTok Influencers, inda suka rika rera wakoki da dauke kwalaye masu dauke da sakonnin goyon baya.
Asali: Legit.ng