2027: Fastocin Takarar Shugaban Ƙasar Gwamnan PDP Sun Mamaye Birnin Kano
- Yayin da siyasa ke ƙara kankama gabanin zaɓen 2027, fastocin gwamnan Oyo, Seyi Makinde sun mamaye wurare da dama a jihar Kano
- Jama'a sun wayi gari da fastocin gwamna Makinde na takarar shugaban kasa, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce
- Wata ƙungiyar matasa 'NYAG Makinde 2027' ta bayyana cewa ta gamsu da shugabancin Makinde, shiyasa ta fara kamfe tun yanzu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Fastocin kamfen takarar shugaban ƙasa na gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde sun mamaye tituna da wasu muhimman wurare a Kano.
An ruwaito cewa an wayi garin yau Alhamis da fastocin kamfen gwamnan na jam'iyyar PDP, waɗanda ke nuna Makinde zai nemi kujerar shugaban kasa a 2027.

Asali: Facebook
Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa fastocin na ɗauke da rubutun, "Don ci gaban Najeriya a 2027," tare da hoton Gwamna Makinde.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wuraren da aka manna fastocin Makinde
An ga fastocin a wuraren da jama’a ke hada-hada kamar kewayen filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA), yankin Wapa da gadar Dangi.
An kuma ga hotunan gwamnan a kasuwar Kwari da ke tara mutane a garin Kano.
Wata ƙungiyar matasa mai suna Nigeria Youths Awareness Group Makinde 2027 (NYAG Makinde 2027) ce ke jagorantar wannan manna fastocin domin tallata gwaninsu.
Kungiyar ta ce suna ta tara mutane a Arewacin Najeriya domin goyon bayan takarar Makinde a zaben shugaban ƙasa mai zuwa idan ya amince ya fito.
Me yasa matasa ke tallata Gwamna Makinde?
Sakataren ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Lawal Abdullahi, ya shaidawa manema labarai a Kano cewa sun kammala tattaunawa da shugabannin siyasa daban-daban a faɗin ƙasar nan.
“Mun zauna da ƙungiyoyi daban-daban kuma mun amince mu haɗa kai domin tallata Seyi Makinde a matsayin ɗan takara a 2027," in ji shi.
Ya ƙara da cewa tuni kungiyar ta tanadi abubuwan kamfe kamar fastoci, allunan talla, takardun talla da sauran kayan talla masu tambari kuma za su bazu a faɗin Arewacin Najeriya, rahoton Vanguard.
Za a ƙara yaɗa fastocin a jihohin Arewa
Lawal ya ƙara da cewa:
“A mako mai zuwa, Insha Allah, za ku ga Kano, Katsina, Jigawa, Borno, Yobe da Gombe sun cika da hotunan Makinde. Jihohin Kudu za su biyo baya."
Lawal Abdullahi ya jaddada cewa ayyukan Gwamna Makinde a Jihar Oyo ne suka janyo masa girmamawa a ƙasa baki ɗaya.

Asali: Facebook
“Mun bi aikin da ya ke yi da kyau kuma mun ga cewa shi shugaba ne mai hangen nesa, mai kishin jama’a. Shi ne irin shugaban da Najeriya ke bukata a yanzu."
Wannan fastoci sun jawo ce-ce-ku-ce daga mazauna birnin Kano, wasu sun bayyana hakan a matsayin ci gaba mai kyau, yayin da wasu suka ce fara kamfen da wuri ya nuna za a fafata a zaben 2027.
Wani mazaunin Kano kuma ɗan kasuwa a Kwari, Isah Ahmad ya shaida wa Legit Hausa cewa ya ga fastocin amma ba za su ce komai ba sai Allah Ya ba mai rabo sa'a.
"Wasu matasa ne haka suka zo suka liƙa su, ni gani nake duk ƴan zauna gari banza ne da ba su da aikin yi, amma garin Kwankwaso ka zo kana tallar wani ɗan takara, ɓata wa kai lokaci ne.
"Muna tare da mai gida kuma shi za mu zaɓa, idan kuma ya ce mu zaɓi wani shi ya hakura, to za mu bi umarninsa," in ji shi.
Gwamna Makinde ba zai bar PDP ba
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya jaddada cewa yana nan daram a jam'iyyar PDP duk da rigingimun cikin gida da suka addabe ta.
Gwamnan ya bayyana cewa ba shi da niyyar barin babbar jam'iyyar adawa ta PDP duk da yadda shugabannin jam'iyya ke sauya sheka a halin yanzu.
A cewarsa, har yanzu PDP tana da ƙarfi kuma za ta ci gaba da wanzuwa sabanin waɗanda ke hasashen za ta rushe nan kusa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng