'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Kogi, Sun Sace Babban Jami'in Soja da Ya Yi Ritaya

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Kogi, Sun Sace Babban Jami'in Soja da Ya Yi Ritaya

  • 'Yan bindiga sun sace tsohon Manjo, Joe Ajayi mai shekaru 76 a gidansa da ke Odo-Ape, Kabba-Bunu, jihar Kogi, a daren ranar Laraba
  • Maharan sun mamaye yankin, tare da bude wuta ta ko ta ina, kafin su yi awon gaba da tsohon sojan da ke fama da rashin lafiya
  • Garkuwar da aka yi da Manjo Ajayi ta jefa al’umma cikin fargaba, tare da ƙara tabbatar da gargadin da kungiyar ci gaban Okun (ODA) ta yi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kogi - 'Yan bindiga sun sace wani Manjo Joe Ajayi (mai ritaya), mai shekaru 76, daga gidansa da ke Odo-Ape, karamar hukumar Kabba-Bunu a jihar Kogi.

An rahoto cewa Manjo Ajayi ya kasance tsohon shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen ƙaramar hukumar Kabba-Bunu.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon manjo din soja a gidansa da ke jihar Kogi
Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo. Hoto: @OfficialOAU
Asali: Facebook

'Yan bindiga sun sace tsohon manjo din soja

Rahoton Channels TV ya nuna cewa 'yan bindigar sun yi garkuwa da Manjo Ajayi da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa maharan sun mamaye yankin, kuma sun shafe fiye da awa ɗaya suna harbe-harbe kafin su yi awon gaba da tsohon sojan zuwa inda ba a sani ba.

Al’ummar yankin sun nuna matuƙar damuwa kan halin da Manjo Ajayi yake ciki, musamman la'akari da cewa yanzu ya tsufa, ba lallai ya jure azabar 'yan ta'addar ba.

Sace tsohon hafsan ya ƙara haifar da fargaba a cikin al’ummar da ke zaune a wannan yaki, tare da kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan tsaro cikin gaggawa.

An taba sace babban sarki a yankin Okun

Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan ƙungiyar ci gaban Okun (ODA) ta nuna damuwarta kan yadda matsalar rashin tsaro ke ƙaruwa a yankin Okun.

ODA ta ce a baya an sace wani sarkin gargajiya mai daraja ta ɗaya a garin Okoloke, da ke karamar hukumar Yagba ta Yamma, inji rahoton The Cable.

A wancan lokacin, kungiyar ta yi gargadin cewa idan gwamnatin tarayya da ta jiha, da ma hukumomin tsaro ba su dauki matakan gaggawa ba, to matsalar tsaro na iya ta'azzara.

Garkuwa da Manjo Joe Ajayi (mai ritaya), ya ƙara tabbatar da abin da ODA ke tsoro, tare da barin jama’ar yankin cikin tsananin firgici da damuwa.

'Yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen mutane a jihar Kogi
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Kogi, wadda ke a shiyyar Arewa ta Tsakiya. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ana samun karin sace-sacen mutane a Kogi

A farkon wannan shekara ma, an sace wani dan ƙaramar hukumar daga gidansa, sannan bayan kwanaki kaɗan, aka sace wasu mutane uku da yaro daya a cikin gona, wanda ya fito da yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a yankin.

Haka zalika, a karo na uku cikin kwana bakwai, 'yan bindiga sun sake kai hari a garin Okoloke da ke karamar hukumar Yagba ta Yamma, inda suka sace mutane huɗu.

Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun kutsa cikin gidan Ezekiel Durojaiye, wani tsohon ma’aikaci kuma dattijon ƙauye daga garin Okunran, inda suka yi awon gaba da shi.

'Yan bindiga sun sace malaman coci a Kogi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun sace fastoci uku a garin Ejule da ke jihar Kogi bayan sun kammala wa’azi, inda suka nemi N20m a matsayin kudin fansa.

Daya daga cikin fastocin da aka sace, akwai Evang. Gabriel Onaji, wanda tsohon limamin cocin garin ne, kuma an tsinci motarsu a wurin da lamarin ya faru.

Rundunar ‘yan sanda ba ta fitar da cikakken bayani ba kan harin, yayin da mazauna yankin ke kira ga gwamnati da ta dauki matakin kubutar da su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.