"Kamar Dole": Yadda Gwamnan PDP Ya Amsa da 'Amin' Lokacin da Aka Yiwa APC Addu'a
- Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya kai ziyara jihar Osun inda ya halarci taro a jami'ar jihar watau UNIOSUN
- Da ya kai ziyara gidan gwamnatin Osun, Gbajabiamila ya yi raha da Gwamna Ademola Adeleke na PDP kan ci gaban jam'iyyar APC
- Hadimin shugaban ƙasar ya sanya Adeleke cewa Amin a lokaci da ya yi addu'ar ci gaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun - Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da karfi da yaɗuwa a lungu da saƙo saboda namijin ƙoƙarin ƴaƴanta.
Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yi addu'ar Allah ya ƙara ɗaukaka APC domin ta kara karfi kuma ya buƙaci Gwamna Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP ya amsa da Ameen.

Asali: Twitter
The Cable ta ce lamarin ya faru ne lokacin da Gbajabiamila ya kai ziyarar girmamawa ga Gwamna Ademola Adeleke a gidan gwamnati da ke Osogbo, babban birnin jihar Osun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Gwamna Adeleke ya amsa da Amin
Yayin da yake jawabi ga gwamnan na PDP, hadimin shugaban ƙasa, Gbajabiamila ya gabatar da addu’a domin cigaban APC, inda ya bukaci Adeleke da ya ce "Amin".
“Ina so zan yi addu’a, kuma ina so in ji amsarka da karfi. Saboda aikin da kake yi a Osun, Allah ya sa APC ta ci gaba da karfi da yaɗuwa. ka ce Amin.”
Sai dai Gwamna Adeleke ya yi jim, bai amsa da wuri ba har sai da Femi Gbajabiamila ya ƙara cewa, “Mai girma Gwamna, ban ji amsarka ba.”
Daga nan, Gwamna Adeleke ya amsa cikin dariya:
“Amin, ai dukanmu daya ne.”
Cikin raha, Femi Gbajabiamila ya ƙara da cewa:
“Hakan dai nake nufi, dukanmu daya ne."
Hadimin Tinubu ya yabi gwamnan Osun
Tun farko, Gbajabiamila ya yaba wa Adeleke da mambobin majalisar zartarwarsa bisa abin da ya kira aiki na ban al’ajabi da suke yi a jihar Osun.
Tsohon kakakin Majalisar Wakilan ya faɗi haka ne kafin ya gabatar da jawabinsa a lakcar shekara-shekara da Jami’ar Jihar Osun (UNIOSUN) ta shirya.
Gbajabiamila ya ce Adeleke ya sanya jagoranci a gaba maimakon siyasa wajen mu’amalarsa da gwamnatin tarayya.

Asali: Twitter
Ya kuma yabawa wakilan jihar a majalisar tarayya, musamman Bamidele Salam, shugaban kwamitin majalisa kan asusun gwamnati, wanda ya ce yana taimaka wa gwamnatin APC wajen toshe cin hanci.
A karshe, Femi Gbajabiamila ya nuna godiyarsa bisa kyakkyawar tarbar da Gwamna Adeleke ya yi masu.
A ranar 1 ga Mayu 2025, Gwamna Adeleke ya musanta jita-jitan cewa zai fice daga PDP zuwa APC, yana mai cewa yana nan daram a jam’iyyarsa.
Sanatocin Osun sun koma bayan Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa sanatocin PDP uku da suka fito daga jihar Osun sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Bola Ahmed Tinubu.
Sanatocin sun ayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa da za su marawa baya a zaben 2027.
Sun tabbatar da cewa ba za su yi ƙasa a guiwa ba wajen ba Tinubu cikakken goyon baya saboda tsarin da ya zo da shi a gwamnatinsa ya kawo saukin rayuwa ga al'umma.
Asali: Legit.ng