An Zo Wajen: Majalisar Amurka Ta Umarci Trump Ya Janye Sojoji a Yaki da Iran

An Zo Wajen: Majalisar Amurka Ta Umarci Trump Ya Janye Sojoji a Yaki da Iran

  • Majalisar wakilan Amurka ta kada kuri’ar umurtar hugaban kasa Donald Trump da ya janye sojojin kasar daga yaƙin da ake yi da Iran
  • An umarci Trump ya janye daga yaƙin ne ko kuma ya nemi amincewar Majalisar dokoki domin ci gaba da rigimar idan an amince masa
  • Hakan ya biyo bayan wasu ‘yan majalisar Republican huɗu da suka mara wa ‘yan Democrat baya, lamarin da ya nuna ƙara adawa da yaƙin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Majalisar wakilan Amurka ta yi sabon suka da ba kasafai ake gani ba ga shugaba Donald Trump, inda ta amince da wani ƙuduri da ‘yan Democrat suka gabatar na kawo ƙarshen yaƙi da Iran, duk da adawar shugabannin Republican.

Wannan na ɗaya daga cikin ƙudurori biyu da ‘yan Democrat suka gabatar waɗanda Fadar White House ta yi adawa da su amma suka samu karbuwa a majalisar da Republican ke da rinjaye.

Kara karanta wannan

Kasar Amurka ta shiga maganar tsare Nnamdi Kanu a Najeriya

Donald Trump a majalisar Amurka
Shugaba Donald Trump na yi wa 'yan majalisar Amurka jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton NBC ya nuna cewa daga baya kuma ‘yan majalisar sun amince da wani mataki da zai ba da damar kada kuri’a kan tura tallafi zuwa Ukraine.

Matakin Majalisar Amurka kan Donald Trump

Ƙudurin ikon yaƙi da Iran wanda ɗan majalisar jihar New York, Gregory Meeks, babban ɗan Democrat a kwamitin harkokin waje, ya gabatar, ya kusa zuwa matakin kada kuri’a kafin majalisar ta shiga hutun a ranar 21 ga Mayun 2026.

Bayan dawowa hutu, a ranar Laraba, ƙudurin ya samu rinjaye da kuri’u 215 kan 208, inda ‘yan Republican huɗu suka haɗa kai da dukkan ‘yan Democrat wajen goyon bayansa.

Su ne Brian Fitzpatrick daga Pennsylvania, Thomas Massie daga Kentucky, Tom Barrett daga Michigan da Warren Davidson daga Ohio.

Ƙudurin ya umurci Trump da ya janye sojojin Amurka daga duk wata arangama da Iran, sai dai idan majalisar dokoki ta ayyana yaƙi ko ta ba da izinin amfani da ƙarfin soja.

Kara karanta wannan

Sabon rikici: Iran ta farmaki sojojin Amurka ganin Trump ya kai mata hari

Yadda aka kaya a majalisa baya

A bana, ‘yan Republican sun yi watsi da wasu yunƙuri uku makamantan wannan ƙuduri. A mafi kusa daga cikinsu, kuri’un sun yi kunnen doki 212 da 212.

‘Yan Democrat sun yi murnar hakan, suna cewa jama’ar Amurka na ƙara juya baya ga yaƙin kuma lokaci ne kawai ya rage kafin su samu nasara.

Kuri’ar da aka kada a ranar Laraba ta ƙara wa ƙudurin ƙarfi a Majalisar dattawa, wadda ta riga ta gabatar da nata ƙudurin ikon yaƙi a watan da ya gabata amma ba ta kai ga kuri’ar ƙarshe ba.

Majalisar dokokin Amurka na zama
Lokacin da Donald Trump ya je Majalisar dokokin Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Business Times ya nuna cewa majalisar dattawa na da ƙarfi fiye da ta majalisar wakilai, domin za ta tilasta wa Trump kawo ƙarshen yaƙin idan bai samu amincewar majalisa ba.

Amurka ta yi magana kan Nnamdi Kanu

A wani labarin, mun kawo muku cewa majalisar dokokin Amurka ta umarci ministan harkokin wajen ƙasar da ya tattauna da Najeriya kan Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Yadda Iran ta haddasa asarar biliyoyin Daloli, ta lalata sansanonin Amurka 20

'Dan majalisar dokokin Amurka John James ya bukaci a matsa wa gwamnatin Najeriya lamba domin tabbatar da cewa an yi wa dan ta'adda, Kanu adalci.

An yanke wa Kanu hukuncin ɗaurin rai-da-rai a ranar 20 ga Nuwamba, 2025 bayan an same shi da laifuffukan ta’addanci da aka zarge shi da su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng