Sunday Igboho Ya 'Gano' Manyan 'Yan Siyasa da ke Daukar Nauyin 'Yan Bindiga a Najeriya
- Fitaccen mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa ne ke daukar nauyin ‘yan bindiga a Najeriya
- Ya ce yana da bayanan wadanda ake zargi da samar da makamai da kudade ga masu aikata manyan laifuffuka na garkuwa da mutane
- Igboho ya yi barazanar cewa zai iya bayyana sunayensu idan har hare-haren da ake kai wa suka ci gaba a sassan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Fitaccen mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa ke daukar nauyin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Najeriya.
Igboho ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin sababbin shugabannin kungiyar daliban Najeriya ta NANS karkashin Akinteye Babatunde a gidansa da ke yankin Soka a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta ce a wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, Igboho ya ce yana da cikakkun bayanai kan wasu mutane da ake zargi da taimaka wa kungiyoyin 'yan bindiga.
Igboho ya yi barazanar fallasa sunaye
Igboho ya yi barazanar cewa idan ba su daina abin da suke yi ba, zai fito fili ya bayyana sunayensu ga jama'a.
A cewarsa:
"Na san ‘yan siyasar da ke bayansu, kuma idan ba su daina ba zan bayyana sunayensu. Su ne ake zargin suna samar musu da harsasai da kudade."
Igboho ya kuma ce ya taba nuna aniyarsa ta taimakawa wajen kubutar da daliban da aka sace a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo, amma gwamnatin jihar ba ta ba shi damar yin hakan ba.
Ya ce daga baya jami'an gwamnati sun sanar da shi cewa masu garkuwa da mutanen sun yi barazanar kashe wadanda suka sace idan ya shiga aikin ceton da kansa.

Kara karanta wannan
Da gaske 'yan bindiga sun sako dalibai da malamai da suka sace a Oyo? Bayanai sun fito
Ana kokarin bata gwamnatin Tinubu
Mai fafutukar ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa na kokarin durkusar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hanyar haddasa rashin tsaro da yada labaran karya.
Ya ce:
"Abin da suka yi wa Jonathan shi suke kokarin yi wa Tinubu. Suna son su sa kasar ta gagara tafiya yadda ya kamata. Suna amfani da farfaganda da labaran karya domin tsoratar da mutane da rage goyon bayan shugaban kasa."

Source: Facebook
Sunday Igboho ya goyi bayan Tinubu
Igboho ya jaddada goyon bayanza ga Shugaba Tinubu, yana mai cewa ba shi da wani dalili na yakarsa a siyasance, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
"Tinubu ne ya taimaka wajen samun ‘yancina lokacin da nake gudun hijira. Ba ni da wani dalili da zan juya masa baya," in ji shi.
Tsaro: An nemi Tinubu ya yi murabus
A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar PRP ta bukaci Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus daga mukaminsa saboda tabarbarewar tsaro a Najeriya.
PRP ta ce gaza wajen sauke babban nauyin da kundin tsarin mulki ya dora masa na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.
Ta kuma nuna matukar damuwa kan yadda makarantu suka zama sababbin wuraren da masu garkuwa da mutane ke kai hare-hare.
Asali: Legit.ng

