2027: Sanatocin PDP Sun Kyale Atiku, Sun Yarda Su Taimaka wa Tinubu Ya Zarce

2027: Sanatocin PDP Sun Kyale Atiku, Sun Yarda Su Taimaka wa Tinubu Ya Zarce

  • Dukkanin sanatocin PDP na Osun sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu, suka ce shi zai zama 'dan takararsu a 2027
  • Sunatocin sun jaddada cewa ayyukan Tinubu sun rage tsadar rayuwa, sun inganta tsaro, kuma suna amfanar da al’umma a mazabunsu
  • Wannan matsaya na zuwa ne a lokacin da rikicin siyasa ke kara kamari a Osun, yayin da kotu ta dawo da shugabannin APC da aka tsige

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gaba daya sanatocin jihar Osun guda uku da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP, sun bayyana goyon bayansu kai tsaye ga Bola Ahmed Tinubu.

Sanatocin sun ayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa da za su marawa baya a zaben 2027 mai zuwa.

Sanatocin jam'iyyar PDP na Osun za su marawa shugaba Bola Tinubu baya a 2027
Shugaba Bola Tinubu ya samu goyon bayan sanatocin PDP na Osun. Hoto: @LereOyewumi, @officialABAT
Asali: Twitter

Vanguard ta rahoto cewa sanatocin sun bayyana matsayarsu ne a wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar a jiya Litinin a Abuja, karkashin kungiyar sanatocin PDP na Osun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Osun: Sanatocin PDP sun marawa Tinubu baya

An ce wadanda suka rattaba hannu kan sanarwar sun hada da Sanata Kamarudeen Lere Oyewumi (PDP, Osun ta Yamma), Sanata Olubiyi Fadeyi Ajagunla (PDP, Osun ta Tsakiya), da kuma Sanata Francis Adenigba Fadahunsi (PDP, Osun ta Gabas).

Sunatocin sun ce za su ba Tinubu cikakken goyon baya saboda tsarin shugabancinsa ya kawo saukin rayuwa ga al'umma, musamman a mazabun da suke wakilta.

Wannan matsaya ta biyo bayan wata ganawa ta dabarun siyasa da sanatocin suka yi a jiya, inda suka yanke shawarar taimaka wa Tinubu ya yi tazarce a 2027.

Sun jaddada cewa suna maraba da ayyukan raya kasa da farfado tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa, wadanda suka fara amfanar da ‘yan kasa.

Dalilin sanatocin na goyon bayan Tinubu

A cewar sanatocin, babban alfanun wadannan ayyuka shi ne raguwar farashin kayan abinci da ingantuwar harkokin tsaro a fadin kasar.

Sun kuma jaddada cewa al'ummar da suke wakiltar na amfanuwa da ayyukan gwamnatin Tinubu, wanda suka kira shugaba mai hangen nesa.

Sun kuma roki shugaban kasar da ya ci gaba da jajircewa wajen ciyar da kasar gaba tare da kawo manyan sauye-sauye da za su amfani al’umma gaba daya.

Sanarwar ta ce:

“Ba wai mun yarda mu goyi bayan Shugaba Tinubu don kawai mun ga ana yi ba ne, mun yi hakan ne bayan gamsuwa da kuma amincewa da muka yi da jagorancinsa.
“Babu wani bambancin siyasa a tsakaninmu. Dukkanin yankin Osun ta Tsakiya za su tsaya tsayin daka wajen goyon bayan wannan kudiri na shugaban kasa.”
Sanatocin Osun guda 3 da aka zaba a PDP sun yanke shawarar marawa Tinubu baya a 2027
Sanatocin Osun: Kamarudeen Lere Oyewumi, Olubiyi Fadeyi Ajagunla da Sanata Francis Adenigba Fadahunsi. Hoto: @LereOyewumi
Asali: Twitter

Rikicin siyasa ya mamaye jihar Osun

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da rikicin siyasa a Osun, inda Gwamna Ademola Adeleke ke takun saka da APC kan zaben kananan hukumomi.

A makon da ya gabata, kotun daukaka kara ta yanke hukuncin dawo da shugabannin APC da aka tsige, abin da ya kara tsananta dambarwar siyasar jihar.

Masu sharhi na ganin cewa goyon bayan da sanatocin PDP suka nuna ga Tinubu na iya zama na muradin kyautata wa al'ummarsu ko kuma dai na kashin kai kawai.

Gwamnan Osun ya magantu kan barin PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya tabbatar da cewa zai ci gaba da kasancewa a jam’iyyar PDP, ba tare da wata niyya ta komawa APC ba.

Adeleke ya bayyana haka ne yayin taron shugabannin jam’iyyar PDP da aka gudanar a fadar gwamnatin Osun da ke Osogbo, babban birnin jihar.

Shugabanni da jiga-jigan jam’iyyar sun nuna farin ciki da wannan matsaya, tare da tabbatar wa gwamnan goyon bayansu kan kokarinsa na sake tsayawa takara a 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.