2027: El Rufai Ya Fara Fuskantar Matsala a SDP bayan Atiku, Obi Sun Zaɓi Jam'iyya
- Ɗan takarar shugaban kasa na SDP a 2023, Adewole Adebayo ya ce jam'iyyarsu ba ta da wakili a tattaunawar haɗakar da ƴan adawa ke yi
- Adebayo ya yi ikirarin cewa ba SDP El-Rufai ke wakilta ba, amma ya tabbatar da cewa jam'iyyar na duba matakan da ya dace ta ɗauka kafin 2027
- Tun bayan samun saɓani da fadar shugaban kasa da APC, tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya tattara ya koma SDP
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa na SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo ya musanta cewa Malam Nasir El-Rufai na wakiltar jam’iyyar a tattaunawar kafa haɗaka gabanin zaben 2027.
Adebayo ya musanta raɗe-raɗin cewa El-Rufai ke wakiltar SDP, yana mai cewa jam'iyyar ba ta shiga wata tattaunawar haɗakar adawa don kifar da APC ba.

Asali: Twitter
Tsohon ɗan takarar ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels ranar Laraba, 21 ga watan Mayu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasir El-Rufai na cikin masu jagorantar haɗaka
Bayan sabani da fadar shugaban kasa, Nasir El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki a watan Maris, sannan ya koma jam’iyyar SDP.
Tun daga lokacin yake yawan kira da neman goyon bayan ’yan adawa da sauran jiga-jigan siyasa domin kafa kawance da nufin karbe mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu da APC a zaben 2027.
Sai dai Adebayo ya nesanta SDP daga wannan yunkuri, yana mai cewa jam’iyyar ba ta shiga kowace tattaunawar kawance da wani mutum ke jagoranta.
SDP ta tura wakili a tattaunawar haɗaka?
Ya kara da cewa shugabancin jam’iyyar SDP bai ba kowa izini ko umarni da ya wakilce ta a irin wadannan tattaunawa ba.
"SDP ba ta cikin kowace haɗaka da wani ke jagoranta. Zan iya tabbatar muku cewa shugaban SDP, Alhaji Shehu Gabam da Olu Agunloye, ba su ba ni izinin shiga wata haɗaka ba, haka kuma ba su ba dan uwana, El-Rufai, izini ba.
"El-Rufai ba ya wakiltar SDP a kowace haɗaka," in ji Adebayo.

Asali: Twitter
SDP na shirin nutsewa cikin haɗakar adawa?
Da aka tambaye shi ko jam’iyyar SDP tana shirin shiga haɗakar, Adebayo ya ce jam’iyyar tana nazari da shirin daukar matakan da suka dace, rahoton Vanguard.
"SDP na jiran lokaci, tana shirye-shirye, tana duba hanyoyi daban-daban da za ta bi don ta hada kai da wasu da nufin kawo karshen mulkin wannan shugaban kasa marar kwarewa da ake kira Bola Tinubu.”
Ya kara da cewa SDP tana da shirye-shiryenta na kanta, tana kuma duba zabin da zai fi dacewa don samar da jam’iyyar da za ta iya tunkarar zabe.
El-Rufai ya fallasa makircin APC
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya zargi APC da haddasa rikici a jam'iyyun adawa kamar PDP da LP.
El-Rufai ya ce babu abin da APC ba za ta iya yi ba domin nakasa jam'iyyun adawa kafin zaben shekarar 2027 da ke tafe.
Ya kuma bayyana cewa da yiwuwar APC ta kunna wutar rikici a jam'iyyar SDP saboda nakasata duba da yadda take ƙara ƙarfi a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng