Kaduna: 'Yan APC Sun Bayyana Dalilansu na Son Uba da Tinubu Su Zarce a 2027
- Jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna ta bayyana cewa tana goyon bayan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani
- Ta ce wannan ya samo asali ne daga yadda gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da hankali wajen kai ayyukan ci gaba ga karkara
- A wani taro da aka gudanar a daya daga cikin kananan hukumomin jihar, sun ce suna son Tinubu da Uba su sake lashe zabensu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Jam’iyyar APC a karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Haka kuma jam’iyyar ta tabbatar da goyon bayanta ga Gwamna Uba Sani, ta nuna cikakken amincewa da ya sake tsayawa takara a zaben 2027 domin neman wa’adin mulki na biyu.

Asali: Twitter
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan mataki ya biyo bayan wani muhimmin taron jam’iyyar da aka gudanar a hedkwatar karamar hukumar da ke Gwantu, inda aka samu halartar jiga-jigai na jam’iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu, Uba sun samu goyon baya a Kaduna
Rahoton ya kara da cewa karamar hukumar Sanga dake yankin Kudancin Kaduna, wuri ne da jam’iyyar adawa ta PDP ke da karfi tun daga 1999 zuwa 2023.
A zaben shugaban kasa na shekarar 2023, PDP ta yi nasara a yankin inda dan takararta, Atiku Abubakar, ya samu kuri’u 445,671, wanda ya kai 40% na jimillar kuri’un da aka kada.

Asali: Facebook
A wani taron APC, wanda ya samu halartar fitattun yan siyasa kamar Mataimakiyar Gwamnan Kaduna, Dr. Hadiza Balarabe, jam’iyyar ta ce karshen adawa ya zo a yankin.
Jam’iyyar ta cimma matsaya, tare da bayyana goyon bayanta ga Shugaba Tinubu da Gwamna Uba Sani, tana mai yabawa da kokarinsu wajen kawo ci gaba da aiwatar da manufofi masu amfani.
Kaduna: An yabi ayyukan Gwamna Uba
A lokacin da take jawabi a wurin taron, Mataimakiyar Gwamna ta yaba da irin sauyin ci gaba da yankin Sanga da sauran yankunan karkara ke samu a karkashin mulkin Gwamna Uba Sani.
Dr. Hadiza ta bayyana cewa Gwamnan ya fi mayar da hankali kan ci gaban yankunan karkara, ta kawo misali da aikin titin Sanga-Jema’a da ake ginawa a yanzu.
Ta ce:
“Za mu gane yadda gwamna Uba Sani ya mayar da kan ci gaban karkara ta cikin ayyuka kamar aikin titin Sanga-Jema’a, wanda zai karfafa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.”
Gwamnan Kaduna ya soki 'yan adawa
A baya, mun wallafa cewa gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ƙalubalanci Nasir El-Rufai, da sauran ‘yan siyasa da ke shirin haɗa kai domin kawar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Yayin wata tattaunawa a ranar Litinin, 3 ga watan Fabrairu, 2025, ya bayyana cewa ya yi mamaki yadda wasu daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC yanzu ke sukar gwamnatin.
Wannan na zuwa bayan da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da El-Rufai suka rika caccakar shugaba Tinubu, inda El-Rufai ya zargi jam’iyyar APC da watsi da manufofinta na asali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng