2027: Alƙawuran da Ake Zargin APC na Yiwa Gwamnonin Adawa saboda Tazarcen Tinubu

2027: Alƙawuran da Ake Zargin APC na Yiwa Gwamnonin Adawa saboda Tazarcen Tinubu

  • Ana zargin jam’iyyar APC na tuntubar gwamnoni na jam’iyyun adawa da alkawarin mukamai da damar zaben yan takara a 2027
  • Atiku Abubakar ya gargadi ’yan adawa kada su mara wa Bola Tinubu baya, yana cewa hakan daidai yake da yarda da gazawar gwamnatin APC
  • Jam’iyyun PDP, NNPP da LP na fama da rikice-rikice na cikin gida, wanda ya haddasa sauya sheka da dama zuwa jam’iyya mai mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tun kafin zaben shugaban kasa na 2027, ana zargin jam'iyyar APC mai mulki da shirye-shiryen yaudarar yan siyasa.

Rahotanni sun ce APC na ci gaba da tattaunawa da gwamnoni na yan adawa tare da yi musu tayin mukamai.

Ana zargin APC da zargin taso yan adawa
An ce APC na alkawura ga yan adawa. Hoto: Atiku Abubakar, Rabi'u Musa Kwankwaso, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Ana zargin APC da yin alkawura ga gwamnoni

Hakan ya jefa damuwa a bangaren Atiku Abubakar, Peter Obi, PDP, NNPP da sauran ‘yan adawa masu shirin tsayawa takara, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi daga APC da jam’iyyun adawa sun tabbatar cewa an yi wa tsofaffin gwamnoni tayin ministoci, da kuma gwamnoni samun damar zabar ‘yan majalisa.

Saboda wannan alkawari, Atiku ya gargadi ‘yan adawa cewa mara wa Tinubu baya a 2027 daidai yake da goyon bayan gazawar gwamnati.

Ya bukaci su hada kai da shi a wani shirin hadin gwiwa da nufin kifar da gwamnatin APC mai ci a zaben 2027.

PDP, NNPP sun tabbatar da zargin da ake yi

Kakakin PDP, Debo Ologunagba, da na NNPP, Ladipo Johnson, sun ce ana tilasta wa mambobinsu shiga APC ta hanyar amfani da karfin gwamnati.

Ologunagba ya dage cewa Tinubu zai fuskanci hukuncin jama’a a 2027, yana mai cewa masu sauya sheka ba za su kare shi ba.

APC ta ƙaryata zarginta kan tuntubar yan adawa
Ana zargin APC da yaudarar yan adawa kan zaben 2027. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

APC ta ƙaryata zargin da ake yi mata

Amma sakataren jam'iyyar APC na kasa, Ajibola Basiru da daraktan yada labarai, Bala Ibrahim, sun musanta zargin cewa ana tilasta wa mutane shiga APC.

Sun ce mutane na shiga APC don son ransu, kuma jam’iyyar na maraba da karin mambobi tare da kare muradunsu da walwalarsu.

Jam’iyyun PDP, NNPP da LP na fama da rikicin cikin gida, wanda hakan ya sa wasu mambobi suka fice zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Rahotanni sun ce fitattun mutane irin su tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, Gwamna Abba Kabir Yusuf na goyon bayan Tinubu a boye.

Sauran wadanda ake zargin suna ciki akwai Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa da Caleb Mutfwang na Plateau.

PDP ta magantu kan hadakar Atiku, Obi

A wani labarin jam'iyyar PDP a Najeriya ta hango yadda Atiku Abubakar, Peter Obi da Nasir El-Rufai za su lashe zaɓen 2027.

Mataimakin shugaban matasan PDP, Hon. Timothy Osadolor ya ce idan manyan yan adawa uku suka cire son rai, za su kawo sauyi a 2027.

Osadolor ya ce idan aka haɗa kuri'un da Atiku da Obi suka samu a zaɓen 2023, za a gane ƙarfin tasirin da haɗakar za ta yi a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.