Kano: Kungiyar Kwankwasiyya Ta Gargadi Abba, Ta Nemi Korar Wasu Jami'ai
- Wata kungiyar Kwankwasiyya ta bayyana damuwa kan yadda wasu mambobin majalisar zartarwa ke gudanar da ayyukansu ba bisa tsarin Abba Kabir Yusuf ba
- Shugaban kungiyar na ƙasa, Kwamared Dayyib Hassan Ahmad, ya fitar da wata sanarwa yana mai cewa wasu na cikin majalisar suna da wata manufa ta daban
- Kungiyar ta bukaci Abba Kabir da ya kula da wadanda ba su taka rawar gani wajen nasarar mulkinsa, tana mai cewa su na neman kudi ne kawai ba cigaba ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Wata ƙungiyar Kwankwasiyya ta yi kira ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya yi taka-tsantsan da wasu da ta kira 'yan-miya-ta-yi-dadi a majalisar zartarwarsa.
Kungiyar ta bayyana cewa wasu daga cikin masu rike da mukamai a cikin gwamnati na da wasu manufofi daban da na gwamna Abba Kabir Yusuf.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sanarwar ta fito ne daga shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Kwamared Dayyib Hassan Ahmad.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta bayyana cewa ya zama wajibi a gare ta ta fitar da wannan gargadi duba da yadda ake gudanar da ayyuka cikin gwamnati.
Gargadin 'yan Kwankwasiyya ga Abba Kabir
Kungiyar ta koka kan zargin rashin damawa da mutanen da suka bayar da gudunmawa wajen cin nasarar NNPP a jihar Kano.
Daily Post ta wallafa cewa sanarwar ta ce:
“Yadda wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwa ke tafiyar da ayyukansu ba ya da nasaba da muradin gwamnan na ganin an samar da ci gaba ga Kano da mutanenta.”
Kungiyar ta ce akwai bukatar duba kan wadanda ke cikin majalisar domin akwai wasu da ke gudanar da ayyuka bisa muradunsu, ba tare da la’akari da manufar Kwankwasiyya ba.
Zargin rashin damawa da 'yan Kwankwasiyya
Kungiyar ta yi zargin cewa akwai wadanda suka sha wahala a tafiyar NNPP a Kano amma ba a damawa da su.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“Abin takaici ne ganin cewa mutane da suka yi bakin kokarinsu wajen nasarar jam’iyyar NNPP da gwamnatin Abba Kabir Yusuf sun rasa kulawa,
"Alhali wasu da ba su taimaka da komai ba suna cikin gwamnati suna fantamawa.”
An nemi Abba Kabir ya kori wasu jami'ai
Kungiyar ta bayyana cewa ko da yake suna tare da Kwankwasiyya da kuma jam’iyyar NNPP, ya kamata gwamna Abba Kabir ya fitar da wadanda ba su taka rawar gani a nasarar tafiyarsa.
Sanarwar ta jaddada cewa ya kamata a dama da mutanen da suka sadaukar da lokaci da dukiyarsu wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023.

Asali: Facebook
Kungiyar ta ce za ta ci gaba da bibiyar abubuwan da ke faruwa a cikin gwamnati domin tabbatar da cewa an cika burin Kwankwasiyya na kawo sauyi mai amfani a jihar Kano.
NNPP ta ba da hakuri kan maganar Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa tsagin NNPP ya ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu hakuri kan kalaman Rabiu Musa Kwankwaso.
Jam'iyyar ta ce Sanata Kwankwaso ya fadi abubuwa da ba su dace da tafiyarsu ta NNPP ba a kan shugabanni.
Baya ga haka, ta bayyana cewa ta sallami Kwankwaso tun da dadewa saboda haka bai kamata a jingina maganarsa ga NNPP ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng