NNPP: Barau Ya Karbi Matan Kwankwasiyya zuwa APC a Abuja

NNPP: Barau Ya Karbi Matan Kwankwasiyya zuwa APC a Abuja

  • Wasu shugabannin mata daga karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano sun sauya sheka daga NNPP zuwa jam’iyyar APC mai adawa a jihar
  • An karɓi matan a ofishin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin tare da shugaban kwamitin kula da lafiya, Sanata Ibrahim Lamido
  • Shugabanin matan sun bayyana rashin adalci da rikice-rikicen cikin gida a jam'iyyar NNPP a matsayin dalilin barin tafiyar Kwankwasiyya

Editan Legit Hausa IbrahYusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Wasu shugabannin mata na jam’iyyar NNPP daga ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar tare da sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

An karɓi matan ne a ofishin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibrin a jiya Litinin.

Barau
Sanata Barau ya karbi matan NNPP zuwa APC. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan sauya shekar ne a cikin wani sako da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPP: Matan Kwankwasiyya sun koma APC

Sanata Barau Jibrin ya karbi wasu shugabannin matan tafiyar Kwankwasiyya zuwa APC a birnin tarayya Abuja.

Shugabannin matan, waɗanda suka haɗa da fitattun jagororin unguwanni, sun samu rakiyar ɗan kasuwa kuma gogaggen mai tunkarar jama’a a matakin ƙasa, Hon. Murtala Maikifi.

Sun bayyana ficewarsu daga jam’iyyar NNPP da kuma Kwankwasiyya bisa la’akari da abubuwan da suka ce ba su dace ba da ke faruwa cikin jam’iyyarsu.

A yayin karɓarsu, Sanata Barau I Jibrin ya ce sun yi zabi mai kyau da suka shiga jam’iyyar APC, wanda ke bai wa kowane mamba damar bayyana ra’ayinsa da samun dama.

Barau ya karbi matan NNPP zuwa APC

Sanata Barau ya samu rakiyar abokin aikinsa, Sanata Ibrahim Lamido, wanda shi ne shugaban kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da lafiya wajen karɓar shugabannin matan.

Mai ba Sanata Barau shawara kan harkokin mata, Hajiya Yardada Maikano Bichi, ce ta jagoranci sauya launin mayafin shugabannin daga ja zuwa fari a matsayin alamar sauya jam’iyya.

Shugabar mata ta Mariri, Hajiya Fadi Dahiru Farawa, ta ce sun fice daga NNPP ne saboda rashin adalci da rikicin cikin gida.

Hajiya Fadi Dahiru Farawa ta ce rikicin na ci gaba da janyo wa jam’iyyar koma baya a matakin ƙasa da jihohi.

Barau
Barau ya yi wa matan NNPP da suka moma APC alakwarin tafiya tare da su. Hoto: Barau I Jibrin
Asali: Twitter

Barau ya ce APC za ta girmama matan NNPP

Sanata Barau ya tabbatar wa sababbin mambobin jam’iyyar cewa za a yi mu’amala da su cikin mutunci, kamar yadda APC ke yi wa mambobinta gaba ɗaya.

A 'yan kwanakin nan dai ana samun masu sauya sheka daga jam'iyyu daban daban yayin da siyasar Kano ke kara daukar zafi.

Sule Lamido ya ce Ganduje zai bar APC

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce nan gaba kadan rikici zai barke a APC.

Sule Lamido ya bayyana cewa masu sauya sheka zuwa APC za su gaza daidaita tsakaninsu wanda hakan ne zai kawo sabani a jam'iyyar.

Baya ga haka, Sule Lamido ya ce shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje zai dawo PDP idan rikicin ya barke.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng