Kano: Gangar Siyasar 2027 Ta Fara Zaƙi, An Nemi Barau Ya Yi Takarar Gwamna da Abba

Kano: Gangar Siyasar 2027 Ta Fara Zaƙi, An Nemi Barau Ya Yi Takarar Gwamna da Abba

  • Kungiyar matasa baƙi mazauna Kano ta bayyana takaicin yadda gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware kungiyoyin da ba na asalin jihar ba
  • Haka kuma ta zargi gwamnatin da daukar wasu matakai da suka jefa rayuwar talakawa a cikin wahala, tare da neman mafita kafin zaben 2027
  • A sanarawar da Sakataren kudi na kungiyar, Malam Usman Abdullahi, ya fitar a Kano, ya ce akwai bukatar Sanata Barau Jibrin ya kawo dauki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kungiyar matasa baƙi mazauna Kano, wato Kano Non-Indigenous Youths Assembly (KNIYA), ta bukaci Barau Jibrin da ya bayyana aniyar ta tsayawa takarar gwamna a jihar a zaben 2027.

Kungiyar ta bayyana cewa tana da yakinin cewa Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin na da nagartar da ake bukata domin dawo da martabar jihar Kano.

Barau
An nemi Barau ya fito takarar gwamnan Kano Hoto: Barau I Jibrin
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa wannan bukata ta fito ne daga wata sanarwa da Sakataren Kudi na kungiyar, Malam Usman Abdullahi, ya fitar a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin neman Barau ya yi takarar gwamnan Kano

The Nation, ta wallafa cewa kungiyar KNIYA ta bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ta gaza, tana mai zargin ta da rushe gine-gine ba bisa ka’ida ba da jefa jama'a a wahala.

Sun kara da cewa matsalolin da jihar ke fama da su sun hada da yadda ake tafiyar da dukiyoyin jihar rashin ci gaban ababen more rayuwa, da karuwar rashin tsaro.

Kungiyar ta nuna damuwarta game da yadda ake watsi da manufofin tallafawa matasa, durkushewar tattalin arziki da kuma yadda jami’an gwamnati ke watsi da ci gaban jama'a.

Kungiyar KNIYA ta soki gwamnatin jihar Kano

Kungiyar ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda gwamnatin jihar ke ware wasu ƙungiyoyi da ba 'yan asalin jihar ba, duk da irin gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban Kano.

KNIYA ta jaddada goyon bayanta ga shirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana kuma kira ga matasan Kano da su hade guri guda domin samar da Kano da kowa zai mora.

Barau
Ana ganin Sanata Barau ne kawai zai iya kawo ci gaba a Kano Hoto: Barau I Jibrin
Asali: Facebook

Kungiyar ta bukaci Sanata Barau da ya saurari kiran da jama'ar jihar Kano da su ke yi masa, tare da bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kano a shekarar 2027.

Ta ce tana da tabbacin cewa jagorancin Sanata Barau zai kawo sabon salo na shugabanci mai ma’ana, gogewa da hangen nesa domin kafa sabuwar Kano.

Gwamnan Kano ya ji koken jama'a

A baya, mun wallafa cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da tallafin abinci da kayan more rayuwa ga fursunoni da ke manyan cibiyoyin gyaran hali guda uku a jihar.

Wannan tallafi ya kunshi kayan masarufi da na walwala domin inganta rayuwar wadanda ke tsare a Kurmawa, Janguza da kuma Goron-Dutse bayan koken jama'a kan halin da ake ciki.

An gabatar da tallafin ne a hukumance a cibiyar gyaran hali ta Kurmawa, inda kwamishinan jin ƙai da rage talauci na jihar Kano, Hon. Adamu Aliyu Kibiya, ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.