Wike na Shirin Neman Takarar Shugaban Ƙasa da Tinubu a 2027? An Samu Bayanai

Wike na Shirin Neman Takarar Shugaban Ƙasa da Tinubu a 2027? An Samu Bayanai

  • Ministan Abuja, Barista Nyesom Wike, ya yi magana kan yaɗa jita-jitar cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027
  • Wike ya ƙaryata rade-radin inda ya ce ba zai taba zai fafatawa da Bola Tinubu ba a babban zaben da ke tafe nan da shekara biyu
  • Ya kara da cewa babu wani dan adawa da zai iya kayar da Tinubu a 2027, yana mai cewa, su zo su tura tikitin wani yanki tukuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan ƙarairayi da ake yaɗawa kan takarar shugaban kasa.

Wike ya karyata rade-radin cewa yana shirin neman tikitin shugaban kasa domin fafatawa da Bola Tinubu a 2027.

Wike ya magantu kan kalubalantar Tinubu a 2027
Wike ya ƙaryata yin takara da Tinubu a 2027. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan ya fadi haka ne a wata hira da yan jaridu da Punch ta bibiya a yau Asabar 17 ga watan Mayun 2027 da muke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Nyesom Wike ya bijirewa PDP a 2023

Tun a shekarar 2023 Wike ya nuna goyon baya ga APC inda ya marawa Tinubu baya a zaben da aka gudanar.

Duk da kasancewarsa ɗan PDP, Wike ya yi kunnen uwar shegu wurin bin Tinubu har ya samu nasara a zaɓen.

Bayan kafa gwamnati, Bola Tinubu ya nada Wike a matsayin ministan Abuja wanda hakan ya jawo ka-ce-na-ce musamman daga ƴaƴan PDP.

Ana rade-radin cewa idan jam’iyyar PDP ta yarda ta bai wa yankin Kudu tikitin shugaban kasa, Wike zai shiga takarar.

Wike ya yi magana kan takara da Tinubu
Wike ya musanta labarin kalubalantar Tinubu a 2027. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike.
Asali: Facebook

2027: Wike ya caccaki masu yaɗa jita-jita

Wike ya nuna damuwa kan jita-jitar inda ya ce ba zai tsaya takara da shugaban da yake aiki a karkashinsa ba wanda ya dauki hakan a matsayin cin amana.

Da aka tambaye shi ko zai tsaya takara idan PDP ta bai wa Kudu dama, Wike ya yi fatali da hakan inda yake cewa akan meye ma zai fara daukar wannan mataki.

Wike ya ce:

“Ba zan tsaya takara ba. Me zai sa in tsaya da wanda nake aiki karkashinsa?”

Wike ya magantu kan yiwuwar lashe zaben Tinubu

An sake tambayarsa ko yana ganin Tinubu zai lashe zaben 2027? Wike ya ce babu wani dan adawa da zai iya kalubalantar shugaban, cewar Daily Post.

Ya kara da cewa:

“Su ce za su bai wa Kudu, to su fara bai wa Kudu tukunna. Idan muka isa gadar, za mu san yadda za mu wuce ta."

Ta yi tsami tsakanin masoyan Wike da Fubara

Mun na ku labarin cewa rigima ta barke a taron jin ra'ayin jama'a da aka yi a Port Harcourt tsakanin magoya bayan Nyesom Wike da na dakataccen Gwamna Simi Fubara.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a inda shugaban GDI ya ce su ne suka taimaka wa Fubara dawowa mulki, hakan ya fusata wasu daga cikin mahalarta taron.

Maganganu sun kara rikita taron, inda aka samu hayaniya da musayar yawu har aka sa jami'an tsaro suka shiga tsakani.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.