'Za a Tafka Kuskure': Wike Ya Fadi Yankin da Ya Kamata PDP Ta Tura 'Dan Takararta

'Za a Tafka Kuskure': Wike Ya Fadi Yankin da Ya Kamata PDP Ta Tura 'Dan Takararta

  • Nyesome Wike ya yi gargaɗin kada PDP ta kai tikitin shugaban ƙasa na 2027 Arewa, yana mai cewa hakan zai dakile nasarar jam'iyyar
  • Ya bukaci PDP ta kai tikitin Kudu, saboda ware tikitin 2023 ya haifar da rikici, kuma ya taimaka wajen shan kayen da jam'iyyar ta yi
  • Yayin da Wike ya ce kai tikitin Kudu zai ba jam'iyyar nasara, ana ganin ya fadi haka ne kawai domin hana jam'iyyar ba Atiku Abubakar tikiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi gargaɗi mai tsauri ga jam'iyyarsa, PDP, game da kai tikitin shugaban ƙasa na 2027 zuwa Arewacin Najeriya.

Da yake magana a wani taron manema labarai a ranar 12 ga Mayu, 2025, Wike ya jaddada cewa sake ba ɗan Arewa tikiti, zai zama babban kuskure da zai iya dakile nasarar PDP a 2027.

Nyesom Wike ya nemi jam'iyyar PDP ta kai tikitin takararta zuwa Kudu a 2027
Ministan Abuja, Nyesom Wike. Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

A maimakon haka, Wike ya bukaci jam'iyyar da ta bayyana a fili cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027 zai fito ne daga Kudancin Najeriya, in ji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya sa Wike ya dauki wannan matsaya

A shekarar 2022, shawarar jam'iyyar yin watsi da tsarin ware tikitin da aka saba, 'idan an ba Arewa a yau, gobe sai a ba Kudu', ya haifar da gagarumin rikicin cikin gida.

Duk da buƙatun wasu masu ruwa da tsaki, ciki har da Wike, na ware tikitin zuwa Kudu, PDP ta buɗe takarar nema tikitin ga dukkanin yankuna.

Wannan matakin ne ya baiwa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ɗan Arewa, damar samun tikitin takara a jam'iyyar.

Ko yaya, matakin ya ɓata wa manyan jiga-jigan jam'iyyar rai, ciki har da Wike da wasu gwamnoni huɗu, waɗanda suka ƙi goyon bayan kamfen ɗin Atiku, wanda ya taimaka wajen kayen da PDP ta sha a zaɓen 2023.

Matsalar da PDP za iya samu a zaben 2027

Wike ya yi jayayya cewa ware tikitin takara zuwa Kudu ya dace da yanayin siyasar Najeriya a halin yanzu, yana mai lura da cewa Shugaba Bola Tinubu, ɗan Kudu, a halin yanzu yana riƙe da shugabancin ƙasa.

Ya yi gargadin cewa rashin ware tikitin zuwa Kudu zai iya haifar da kuskuren dabarun cin zabe, musamman idan jam’iyyar APC mai mulki ta canja tikitinta zuwa Arewa a 2031 bayan yiwuwar wa’adin mulki na biyu na Tinubu.

Wike ya soki abin da ya bayyana a matsayin "son kai" da "wayo" a cikin PDP, yana mai cewa irin waɗannan dabarun na iya "kashe tsari" da kuma lalata haɗin kan jam'iyyar.

Ana zargin Wike na son PDP ta kai tikitin takarar 2027 zuwa Kudu don hana Atiku yin takara a jam'iyyar
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar | Ministan Abuja, Nyesom Wike. Hoto: @Atiku, @GovWike
Asali: Facebook

Kai tikitin PDP zuwa Kudu zai hana Atiku takara

Atiku, wanda ya yi takarar shugaban ƙasa akai-akai, ya bayyana a watan Mayu 2024 cewa zai ci gaba da neman cika burinsa na zama shugaban ƙasa muddin yana da koshin lafiya.

Ana ganin cewa, Wike ya nemi PDP ta kai tikitin takararta zuwa Kudu domin hana Atiku tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar a 2027.

Wike, wanda ke aiki a gwamnatin APC amma ya ci gaba da zama mamba a PDP, ya dage cewa yana aiki ne don ƙarfafa jam'iyyar, inji rahoton Leadership.

Koma yaya ne, haɗin gwiwarsa da APC da kuma sukar da yake yi wa shugabancin PDP ya ci gaba da haifar da zarge-zarge game da manufofinsa.

Neman PDP ta kai tikitin ta Kudu da Wike ke yi na iya ƙarfafa goyon baya a Kudu amma a hannu daya hakan zai iya ɓata wa masu ruwa da tsaki na Arewa rai.

'Abin da zai iya faruwa da PDP a 2027' - Wike

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa son zuciya kaɗai na iya ƙarasa kashe jam'iyyar PDP gabannin zaɓen 2027.

Wike, tsohon gwamnan Ribas ya ce alamu sun nuna PDP za ta samu nasara ba a zaɓen 2027 matuƙar abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka.

Ya kuma bayyana sauya shekar tsohon gwamnan Delta kuma abokin takarar Atiku Abubakar a zaɓen 2023, Ifeanyi Okowa a matsayin dabarar siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.