'Ko Yau aka Yi Zabe, Tinubu zai Lashe,' Oshiomhole Ya Bugi Kirji kan 2027

'Ko Yau aka Yi Zabe, Tinubu zai Lashe,' Oshiomhole Ya Bugi Kirji kan 2027

  • Sanata Adams Oshiomhole ya nuna tabbacin cewa idan zaɓe ya gudana a yau, Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai lashe shi cikin sauƙi
  • Ya bayyana haka ne yayin wata hira da aka yi da shi, a nan ya ce shugaban ƙasa ya ɗauki matakai masu kyau domin daidaita Najeriya
  • Oshiomhole ya yi nuni da cewa matakan sun dawo da zaman lafiya a yankunan da manoma ke gudun fita gona sakamakon rashin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Edo kuma Sanata mai wakiltar Edo ta Tsakiya, Adams Oshiomhole, ya ce babu tantama Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu nasara a 2027.

Oshiomhole ya ce nasarorin da Shugaba Tinubu ya samu wajen dakile rashin tsaro da gyaran harkar tattalin arziki na ƙara ƙarfafa masa gwiwa a zukatan 'yan Najeriya.

Oshiomhole
Oshiomole ya ce Tinubu zai lashe zaben 2027. Hoto: Official APC
Asali: Twitter

Sanatan ya fadi haka ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV, a lokacin da ake tattauna batun sauya sheƙar wasu sanatocin jihar Kebbi zuwa jam’iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oshiomhole ya ce Tinubu zai lashe zaben 2027

Yayin da aka tambaye shi ko Tinubu zai yi nasara idan zaɓe ya gudana a yau, Adams Oshiomhole ya ce:

“Zai yi nasara ƙwarai da gaske.”

Oshiomhole ya ce ko a yau aka kada kuri'a a Najeriya Bola Tinubu zai lashe zabe ba tare da tantama ba.

Ya ce ɗaya daga cikin sanatocin da suka dawo APC ya bayyana cewa kafin Tinubu ya hau mulki, mutanen mazabarsa ba su iya fita gona saboda matsanancin rashin tsaro.

Sanatan ya ce yanzu al’ummar yankin sun fara komawa gonakinsu cikin kwanciyar hankali, abin da ya ce yana daga cikin manyan nasarorin gwamnatin Tinubu.

Oshiomhole ya ce Tinubu ya gyara tattali

Adams Oshiomhole ya ƙara da cewa kafin zuwan Tinubu, ana bai wa wasu ƴan tsiraru Dala a farashi mai sauƙi saboda dangantakarsu da gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).

Oshiomhole ya yabawa Tinubu da ya dakatar da wannan tsarin, yana mai cewa yanzu kowa na samun Dala daidai da farashin kasuwa, kuma hakan na da amfani ga al’umma gaba ɗaya.

Tinubu yana aiki ne don cigaba inji Oshiomhole

Oshiomhole ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya kauce wa amfani da damar ofishinsa domin amfana da tsarin canjin kuɗi da wasu suka yi ta amfani da shi.

Bola Tinubu
Oshiomhole ya ce Tinubu ya yi kokari a fannin tsaro. Hoto: Bayo Onanuga|APC Official
Asali: UGC

Ya ce manufar shugaban ƙasa ita ce kawar da duk wata hanya da ƴan tsiraru ke amfani da ita wajen azurta kansu ta hanyoyin da suka sabawa doka.

Ya kuma ƙarfafa cewa irin waɗannan matakan ne ke ƙarfafa jam’iyyar APC da tabbatar da nasarar Tinubu idan aka sake fuskantar zaɓe a nan gaba.

Gwamnan Edo ya yi wa Tinubu kamfen

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Edo ya gana da manyan sarakunan gargajiyan yankin Kudu maso Kudu.

Gwamnan ya roki sarakunan da su goyi bayan shugaban kasa Bola Tinubu domin samun daman zarcewa a 2027.

Ya bayyanawa sarakunan cewa Bola Tinubu ya kawo tsare tsare masu kyau da ya kamata ya karasa a wa'adinsa na biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng