Bwala Ya Yiwa Atiku Shagube, Ya Nuna Yadda ake Gudun Hadakar Adawa da Tinubu

Bwala Ya Yiwa Atiku Shagube, Ya Nuna Yadda ake Gudun Hadakar Adawa da Tinubu

  • Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya ce haɗakar jam’iyyun adawa da ake cewa ana yi kafin zaɓen 2027 ba za ta kai ko ina ba
  • Ya ce manyan yan siyasa da jam'iyyu kamar su PDP da LP sun musanta shiga kowace irin tattaunawar haɗin gwiwa da Atiku Abubakar
  • Bwala ya ce APC ce ke samun karuwa, tana karɓar masu sauya sheƙa daga sauran jam’iyyu, ba haɗakar adawa ba kamar yadda ake ikirari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala, ya ce ikirarin da ake cewa akwai gagarumar haɗakar jam’iyyun adawa da ke tunkaro zaɓen 2027 bai wuce mafarkin wasu yan siyasa ba.

A ranar Alhamis ne Bwala ya karyata rahotannin da ke cewa ana samun karuwar haɗin gwiwar jam’iyyun adawa kafin babban zaɓen 2027, yana mai cewa wannan ba gaskiya ba ne.

Bwala
Hadimin Bola Tinubu, Bwala ya caccaki tsohon ubangidansa, Atiku Hoto: Bwala Daniel/AbdulRasheeth Shehu
Asali: Facebook

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Bwala ya jaddada cewa babu wata jam’iyya ko jigo a siyasa da ta bayyana goyon baya ga hadakar Atiku Abubakar da Nasir El-Rufa’i ne ke jagoranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan PDP na guje wa hadakar Atiku Abubakar

Arise News ta ruwaito Bwala ya bayyana cewa batun haɗin gwiwa tsakanin PDP da LP da sauran jam’iyyun adawa tamkar magana ce kawai da ake yi a jarida, amma babu wannan nasarar.

Bwala ya rubuta cewa:

"Yin iƙirarin cewa haɗakar jam’iyyu na ƙara ƙarfi alhali babu wanda ke sha’awar shiga cikinta, tamkar mafarki ne na siyasa da wasu ke yi."
"Dukkanin gwamnonin PDP da kwamitin gudanarwar jam’iyyar sun bayyana a fili cewa ba su cikin wata tattaunawa ta haɗin gwiwa."
"Haka kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Mista Peter Obi, kwanan nan ya nesanta kansa da irin wannan yunkuri."

Bwala ya yi wa Atiku shagube

Daniel Bwala ya ƙalubalanci ikirarin cewa jam’iyyun adawa haɗa kai, yana mai cewa APC ce ke samun karuwa saboda yawan sauya sheƙa da ake yi zuwa cikinta.

Bwala
Bwala ya ce APC ce ke kan ganiyarta ba hadakar su Atiku ba Hoto: Bwala Daniel
Asali: Facebook

Ya ce:

"Akasin haka, jam’iyyar da ke samun karuwa ita ce APC, tana karɓar sababbin yan jam'iyya ta ko ina. Ba haɗaka ba ce, mafarki ce kawai ta siyasa."

Atiku ya ƙalubalanci Bola Tinubu

A baya, kun samu labarin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki kudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kishin ƙasa.

Atiku, wanda ya nemi takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben 2023 ya kuma bayyana kudirin a matsayin sabuwar farfaganda da ke nufin yaudarar 'yan Najeriya.

A cewarsa, gwamnatin tarayya na ƙoƙarin sa rudani a zukatan jama'a, yayin da shugaban ƙasa ke yawon duniya yana morar duba lafiyarsa a Faransa da Landan, an bar jama'a a wahala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.