Gwamna Sule Ya Fara Juyawa Shugaba Tinubu Baya gabanin 2027? An Samu Bayani

Gwamna Sule Ya Fara Juyawa Shugaba Tinubu Baya gabanin 2027? An Samu Bayani

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya musanta ikirarin cewa ya fara ja baya daga goyon bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Gwamnan ya ce kalaman da ya yi cewa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ne jagoran CPC ba suna nufin goyon bayan wani ɓangare ba ne
  • Wannan dai na zuwa ne bayan shugaban kungiyar ƴan APC na Arewa ta Tsakiya ya zargi gwamnan da fara janye goyon bayansa ga Bola Tinubu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa - Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya jaddada goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma burinsa na zarce wa wa’adi na biyu a zaɓen 2027.

Gwamna Sule ya musanta ikirarin cewa ya fara raba ƙafa game da goyon bayan tazarcen Tinubu, ya ce wannan zargin ba gaskiya ba ne.

Gwamna Abdullahi Sule.
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya musanta zargin raba ƙafa game da goyon bayan Bola Tinubu Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Facebook

Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Addra, ya fitar jiya a Lafia, babban birnin Nasarawa, The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta kasance martani ga Alhaji Saleh Zazzaga, shugaban wata kungiyar ƴan APC ta Arewa ta Tsakiya, wanda ya zargi Gwamna Sule da raba ƙafa game da goyon bayan Tinubu.

2027: Wane zargi ake yi wa Gwamna Sule?

Tun farko Saleh Zazzaga ya ƙaubalanci Gwamna Sule kan kalaman da ya yi a taron ƙungiyar ALGON cewa Muhammadu Buhari ne kaɗai zai yanke inda ƴan CPC za su dosa.

Zazzaga ya bukaci gwamnan ya fito ya bayyana ɓangaren da yake, tsagin Shugaba Tinubu ko magoya bayan Buhari, bai kamata yana raba ƙafa ba.

Da yake mayar da martani, Ibrahim Addra ya bayyana kalaman Saleh Zazzaga a matsayin "munana" wanda ke neman jan hankalin mutane, Leadership ta rahoto.

Gwamna Sule na tare da Bola Tinubu

A sanarwar, mai magana da yawun gwamnan Nasarawa ya ce:

“Gwamna Sule ya jima yana tare da gwamnatin Shugaba Tinubu tun bayan hawansa mulki. Kalaman da ya yi kwanan nan a taron da ALGON ba raba kafa ba ne."

Gwamnan ya ce kiran tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin jagoran tsohuwar jam’iyyar CPC gaskiya ce da kowa ya sani, ba wata manufa ce ta siyasa ba.

“Wanda ya ce Buhari ba shi ne jagoran CPC ba, ya kamata ya fito ya fadi hujjojin da suka sa ya faɗi haka, maimakon rarume a duhu da zargi mara tushe," in ji shi.
Gwamna Sule da Bola Tinubu.
Gwamna Sule ya bayyana koƙarin da yake na haɗa kan ƴan APC Hoto: Abdullahi A. Sule, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Gwamna Sule na ƙoƙarin haɗa kan ƴan APC

Sanarwar ta ce Gwamna Sule ba neman yabo ko mukami yake yi ba, yana ƙoƙarin haɗa kan kowane ɓangare na APC domin ɗorewar zaman lafiya da ƙarfi a cikin gida.

An ji sanarwar ta ce fassarar kalaman Gwamna Sule a matsayin juyawa Shugaba Tinubu baya kuskure ne mara ma'ana da ƙoƙarin canza ainihin ma'anar kalaman.

Gwamnan Nasarawa ya ce Buhari na da tasiri a APC

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana tasirin da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ke da shi a APC yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Abdullahi Sule ya ce kuri'u miliyan 12 na nan tare da Buhari kuma za su yi wa APC amfani a zaɓe mai zuwa.

Sule ya soki masu tunanin cewa Buhari da magoya bayansa za su fice daga hadakar da ta haifi APC, yana mai cewa har yanzu dattijon jagora ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262