Zaben 2027: Gwamna Sule Ya Yi Nasiha kan wanda Zai Gaje Shi
- Gwamnan jihar Nasarawa ya taɓo batun wanda zai gaje shi idan ya kammala wa'adin mulkinsa na shekara takwas a 2027
- Abdullahi Sule ya bayyana cewa ba shi da ikon yanke hukunci kan wanda zai gaje shi idan ya kammala mulkinsa a gidan gwamnati
- Gwamnan na Nasarawa ya nuna cewa Allah maɗaukakin Sarki ne kawai ke da ikon zaɓar wanda yake so ya karbi kujerar shi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan wanda zai gaje shi bayan ya kammala wa'adin mulkinsa.
Gwamna Sule ya bayyana cewa Allah Maɗaukakin Sarki ne kaɗai zai zaɓi wanda zai gaje shi a matsayin gwamna.

Asali: Facebook
The Nation ta ce Gwamna Sule ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, yayin wani babban taron da ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen Nasarawa, ƙarƙashin jagorancin Hon. Safiyanu Isa Andaha, ta shirya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shirya taron ne domin girmama Labaran Shuaibu Magaji PhD bisa naɗa shi a matsayin sakataren gwamnatin jihar Nasarawa.
Me Gwamna Sule ya ce kan wanda zai gaje shi?
Abdullahi Sule ya ce Allah ne yake ba da mulki, kuma shi kaɗai ke da ikon ba da shi ga wanda ya so, a lokacin da ya ga dama.
Ya ce yanke wannan hukunci ya fi ƙarfin sa, domin ikon zaɓar shugaba na hannun Allah ne kaɗai.
Gwamnan ya shawarci mutanen jihar da su jira lokacin da Allah zai zaɓi wanda ya yarda da shi daga cikin fiye da mutane 20 da ke neman takarar kujerar gwamna a zaɓen 2027.
“Wannan matsayi na gwamna, mutum ɗaya ne kaɗai zai same shi, sauran kuwa dole su haɗa kai da wanda Allah ya zaɓa."
"A binciken da na yi, na ga kusan mutum 20 da ke neman wannan kujera ta gwamna a jihar Nasarawa."
"Wannan shi ne abin da na gani. Saboda haka, dole ne a samu haɗin kai, yafiya da kuma aiki tare, idan muna son mu cimma burinmu."
“Domin a ƙarshe, mutum ɗaya ne kawai zai samu wannan kujera. Kuma ina so na bayyana a fili, Allah maɗaukaki ne kaɗai ke bayar da wannan matsayi."
"Wannan matsayi na sakataren gwamnatin jihar Nasarawa ba ni ne na ba shi ba, Allah ne ya ba shi. Haka zalika, Allah ne zai zaɓi wanda zai zama gwamna na gaba, ba ni ba. Saboda haka, ya kamata mu fuskanci wannan lokaci da natsuwa da tawakkali."
- Gwamna Abdullahi Sule

Asali: Facebook
Gwamnan ya kuma nuna godiya ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa goyon bayan da yake bai wa jihar Nasarawa a kai a kai.
Arewa za ta marawa Tinubu baya - Sule
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa yankin Arewa ba zai juyawa Bola Tinubu baya ba.
Gwamna Sule ya bayyana cewa yankin Arewacin Najeriya zai goyi bayan Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.
Hakazalika ya kuma nuna cewa yankin Arewa zai mutunta alƙawarin da ya ɗauka na yankin Kudu ya samar da shugaban ƙasa har na shekara takwas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng