'Arewa na Godiya': Matasan Yankin Sun Yabawa Ministan Tinubu a Bangaren Lafiya

'Arewa na Godiya': Matasan Yankin Sun Yabawa Ministan Tinubu a Bangaren Lafiya

  • 'Arewa Youth Congress' ta goyi bayan sabon shugaban hukumar harkar lura da hakori, DTRBN da cewa yana da nagarta, hangen nesa da kwarewa
  • Kungiyar ta yaba wa karamin Ministan Lafiya, Dr. Iziaq Salako, bisa yadda ya bai wa Arewa shugabanci a hukumomi tara cikin 14 a ma'aikatar lafiya
  • Ta kuma gode wa tsohuwar shugabar hukumar DTRBN, Mercy Ojo, bisa gaskiya da adalci da ta nuna, tare da fifita yankin Arewa a ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Kungiyar 'Arewa Youth Congress' ta yi magana kan samun ci gaba a bangaren lafiya a Najeriya.

Kungiyar ta bayyana goyon bayanta ga sabon shugaban hukumar likitocin haƙora, DTRBN, Dr. Dele Anisere, bayan sauyin shugabanci da aka samu kwanan nan.

An yabawa ministan Tinubu a Arewa
Matasan Arewa sun yabawa ministan Tinubu a bangaren lafiya. Hoto: Federal Ministry of Health.
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar, Ambasada Hassan Sadau Mohammed shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa a yau Litinin 12 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake yabon gwamnatin Tinubu a bangaren lafiya

Al'umma da dama sun yabawa gwamnatin Bola Tinubu musamman karkarshin jagorancin Dr. Muhammad Ali Pate a bangaren lafiya.

A kwanakin baya, ministan ya tabbatar da cewa duk wanda aka ka shi asibiti bangaren hadura da kulawar gaggawa zai samu magani kyauta na tsawon awa 48.

Wannan mataki ya taimakawa masu fama da rashin lafiya musamman marasa ƙarfi wurin rage musu radadin halin da ake ciki.

Harkar lafiya: Matasa sun yabi ministan Tinubu

A yayin taron manema labarai da aka yi a dakin taro na 'Arewa House', Kaduna, kungiyar ta yaba wa Ministan Lafiya, Dr. Iziaq Salako.

Kungiyar ta ce Dr. Salako ya tabbatar da shugabanci mai adalci inda shugabanni tara daga cikin hukumomi 14 na lafiya suka fito daga Arewacin Najeriya.

Kungiyar ta kuma yi godiya ga tsohuwar shugabar hukumar, Mercy Omowunmi Ojo, bisa gaskiya, wakilci da ci gaba da ta samar wa Arewa.

Ta ce mika mulkin cikin lumana da gaskiya da Mercy ta yi, ya zama abin koyi ga sauran shugabanni masu kishin kasa da zaman lafiya.

An yabawa ministan Tinubu a bangaren lafiya
Kungiyar a Arewa ta yabawa ministan Tinubu. Hoto: Hassan Sadau Mohammed, Federal Ministry of Health.
Asali: Facebook

Matasa sun jaddada goyon baya ga shugabanni

Kungiyar ta bayyana cikakken goyon baya ga Dr. Anisere, tana fatan zai jagoranci hukumar cikin adalci, kishin kasa da rikon gaskiya.

Ta kara da cewa:

“Lokaci ne na hadin kai ba rigima ba, muna kiran kowane dan kasa na gari da ya mara wa wannan sauyi baya."

Kungiyar ta kuma yabawa Ministan Lafiya na kasa, Muhammad Ali Pate, saboda tsare-tsaren gyara da dorewar shugabanci da yake nunawa.

A karshe, kungiyar ta jaddada kudurinta na ci gaba da goyon bayan shugabanni da manufofin da ke tallafa wa zaman lafiya da hadin kan kasa.

Shettima ya sha gorin Matasan Arewa

A baya, mun ba ku labarin cewa Kungiyar 'Arewa Ina Mafita' ta soki jagoran kungiyar AYCF, Yerima Shettima kan tsoma baki a harkokin yankin Arewa.

Shugaban kungiyar, Kwamred Nura Hussaini, ya ce Shettima yana amfani da sunan Arewa don biyan bukatunsa, ba don kishin yankin ba.

Kungiyar ta zargi Shettima da cin mutuncin Nasir El-Rufai da wasu ‘yan Arewa domin samun kusanci da Gwamna Uba Sani.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.