Saƙon APC ga Gwamnan PDP bayan Ya Fara Shinshinar Shiga Jam'iyyar

Saƙon APC ga Gwamnan PDP bayan Ya Fara Shinshinar Shiga Jam'iyyar

  • Jam’iyyar APC ta ce a shirye take ta karɓi Gwamna Umo Eno daga PDP bayan ya kwatanta jam’iyyarsa da jirgi mai matsala
  • Mai magana da yawunta APC, Felix Morka ya ce PDP kamar jirgi ne da ba zai iya tashi lafiya ba, yana mai maraba da ra’ayin Eno
  • APC ta tabbatar wa Eno cewa jirginsu na siyasa lafiya yake, tare da ƙwararrun ma’aikata da za su kai shi inda ya ke so
  • PDP ta gudanar da taron gaggawa kan sauya sheƙa, inda aka ba lauyan jam’iyya umarni ya ɗauki mataki kan ‘yan sauya sheƙa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta yi wa Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom alkawari kan shirin shiga cikinta.

Jam'iyyar ta ce dandamalin siyasarta shirye yake don ɗaukar Gwamnan na Akwa Ibom daga PDP mai adawa.

APC ta yi maraba da gwamnan PDP da ke shirin komawa cikinta
APC ta fadi shirinta na karbar Gwamna Umo Eno zuwa jam'iyyar. Hoto: Pastor Umo Eno, All Progressives Congress.
Asali: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da Felix Morka, mai magana da yawun APC ya sanyawa hannu, wanda hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya magantu kan yiwuwar komawa APC

A baya-bayan nan a Akwa Ibom, Umo Eno ya ce jirgin PDP “ba zai iya tashi lafiya ba” yana nuna buƙatar zaɓen wata jam’iyya.

Gwamna Eno ya nuna maganar sauya shekarsa daga PDP zuwa APC na nan tafe kafin 2027.

A wata ganawa da jama’a a Ukanafun, Fasto Eno ya kwatanta PDP da jirgin sama da ya lalace wanda ba zai iya tashi ba.

Hakan ya biyo bayan sauya shekar takwaransa na jihar Delta, Sheriff Oborevwori da tsohon gwamna, Ifeanyi Okowa.

APC tana maraba da gwamnan PDP zuwa cikinta
Jam'iyyar APC ta yi wa Gwamna Umo Eno alkawari yayin da yake shirin shiga cikinta. Hoto: Pastor Umo Eno.
Asali: Twitter

APC tana maraba da gwamna daga PDP

A martaninsa, mai magana da yawun APC ya ce jam’iyyarsu na maraba da kalaman gwamnan, tare da amincewa da ra’ayinsa kan PDP.

Sanarwar ta ce:

“Ba za mu iya musantawa ba cewa jirgin PDP ya zama abin da ba zai iya aiki ko tafiya lafiya ba.
“Tun da lafiya da jin daɗi su ne sharuddan tashi, jam’iyyarmu mai girma na tabbatar wa gwamna cewa jirgin APC shirye yake.
"Yan kwamitinmu masu tuki da ma’aikata ƙwararru ne, masu ƙwarewa, muna masa maraba, da kulawa da cikakken shiri don kai shi inda ya ke so.
“Muna tabbatar wa Gwamna Eno cewa tafiya tare da mu zai zama irin tafiyar da ba zai manta da ita ba.”

APC na fatan ganin Gwamna Umo Eno ya sauya sheƙa zuwa gare ta, bayan kalamansa da suka nuna rashin gamsuwa da PDP.

Tinubu ya yi maganar sauya-sheka a Delta

Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ji dadin guguwar siyasa da ta kunno kai a Najeriya da jiga-jigan PDP suka dawo APC.

Tinubu ya bayyana sauyin jam’iyya daga PDP zuwa APC a Delta a matsayin “guguwar siyasa” mafi girma da aka taba gani.

Gwamna Sheriff Oborevwori da Ifeanyi Okowa sun ce sauyin ya yi daidai da bukatun jihar Delta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.