Tsohon Minista Ya Dawo Gwamnati, Tinubu Ya ba Shi Mukamin Hadiminsa

Tsohon Minista Ya Dawo Gwamnati, Tinubu Ya ba Shi Mukamin Hadiminsa

  • Shugaba Bola Tinubu ya sake yin nadin mukamai a gwamnatinsa bayan maye gurbin wasu ministoci da suka bar kujerarunsu
  • Tinubu ya nada sabon mai ba shugaban kasa shawara kan wutar lantarki tare da jagorantar kwamitin gyaran bangaren
  • Fadar shugaban kasa ta ce an sauya ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan makamashi zuwa mai kula da harkokin mai da iskar gas domin rage rikice-rikice

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Mista Rilwan Lanre Babalola a matsayin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin makamashi.

Hakan ya biyo bayan garambawul a gwamnatinsa da nadin wasu ministoci bayan wasu sun ajiye mukamansu saboda takara.

Tinubu ya nada sabon hadimi a bangaren wutar lantarki
Shugaba Bola Tinubu yana saka hannu a takardu a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a Facebook.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya nada sabon Ministan lantarki bayan Adelabu ya yi murabus

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin ta sauya tsarin kula da bangaren makamashi domin kawo sauyi da inganta ayyukanta.

A cewar sanarwar, an sauya ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan makamashi zuwa mai kula da harkokin mai da iskar gas domin kauce wa maimaita ayyuka.

Sanarwar ta bayyana cewa Babalola, tsohon ministan makamashi, yana da kwarewa sosai wajen fahimtar matsalolin tsarin samar da lantarki da kalubalen bangaren Najeriya.

Tinubu ya nada sabon hadimi kan makamashi a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da sabon hadiminsa, Rilwan Babalola. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Ayyukan da kwamitin zai yi

Kwamitin da zai jagoranta zai kasance karkashin umarnin shugaban kasa kai tsaye domin dawo da inganci, ladabtarwa da bunkasa harkokin kasuwanci a bangaren wuta.

An ce kwamitin zai hada kai tsakanin ma’aikatu da hukumomi wajen aiwatar da muhimman gyare-gyare domin kara samar da lantarki a fadin Najeriya baki daya.

Ayyukan kwamitin sun hada da sake fasalin bangaren lantarki gaba daya, rage asarar fasaha da ta kasuwanci tare da tabbatar da ingancin tsarin kudin wuta.

Hakazalika, kwamitin zai inganta kudaden shiga, karfafa tsarin kasuwanci, dawo da daidaiton layin wuta tare da bunkasa amfani da lantarki wajen habaka tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Atiku ya ce zubar da jinin 'yan Najeriya zai kawo karshen Tinubu a 2027

Sanarwar ta kara da cewa kwamitin zai samar da yankunan bunkasa lantarki tare da rage nauyin kashe kudade ga gwamnati a bangaren samar da wuta.

Fadar shugaban kasa ta ce ana sa ran Babalola zai gudanar da aikin cikin gaggawa, ladabtarwa da mayar da hankali wajen samar da sakamako mai amfani ga ‘yan Najeriya.

Ƙarin bayani na tafe.....

Tinubu ya nada sabon ministan makamashi

Mun ba ku labarin cewa majalisar zartarwa a Abuja ta sake samu sabon Minista biyo bayan nadin Shugaba Bola Tinubu da aka yi a yau Alhamis 30 ga watan Afrilun 2026.

Bola Tinubu ya nada sabon ministan makamashi wanda zai maye gurbin Adebayo Adelabu sakamakon murabus din da ya yi saboda neman takarar gwamna a Oyo.

Shugaban ya dauko Joseph Olasunkanmi Tegbe wanda ya fito daga jihar Oyo, ya ba shi mukamin ministan makamashi na tarayyar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.