Manoma Sun Hada Kudi, Sun Saya wa Gwamna da 'Dan Majalisa Fam din Neman Takara a 2027

Manoma Sun Hada Kudi, Sun Saya wa Gwamna da 'Dan Majalisa Fam din Neman Takara a 2027

  • Manoma sun hada kudi sun saya wa Gwamna Mohammed Bago fam din APC na nuna sha'awar tsayawa takara karo na biyu a jihar Neja
  • Bayan haka, manoman sun kuma saya wa dan majalisar wakilai mai wakiltar Bida/Gbako/Katcha, Hon. Sa’idu Musa Abdullahi fam
  • Sun bayyana cewa wadannan shugabanni biyu sun taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin noma a jihar Neja

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja – Manoma a jihar Neja karkashin kungiyar manoman Najeriya (AFAN) sun bayyana goyon bayansu ga tazarcen Gwamna Muhammed Umaru Bago.

Manoman sun kuma jaddada goyon baya ga 'dan majalisar wakilai mai wakiltar Bida/Gbako/Katcha, Hon. Sa’idu Musa Abdullahi, domin ya sake tsayawa takara a zaben 2027.

Gwamna Bago.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago a fadar gwamnati da ke Minna Hoto: Mohammed Umar Bago
Source: Twitter

Manoma sun sayawa gwamnan Neja fam

Haka kuma, manoman sun sayi fom din nuna sha’awa da na tsayawa takara na jam’iyyar APC ga dan majalisar da Gwamna Bago, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Mulki na Allah ne": Mataimakin shugaban majalisa ya hakura da neman kujerar sanata Ndume

Yayin gabatar da fom din ga dan majalisar a Abuja, manoman sun ce sun dauki wannan mataki ne domin nuna godiya ga irin kulawa da gudunmawar da shugabannin biyu ke bayarwa wajen bunkasa harkar noma a Neja.

A cewar manoman, 'dan majalisar babban jigo ne ga manoman jihar Neja, inda ya dauki matakai da dama da suka saukaka harkokin noma.

Manoma sun yabawa dan Majalisa

Sun ce ya gina tsarin ban ruwa na noman rani a Badegi kuma ya fadada shi zuwa Begi, tare da samar da damammaki ga mata a harkar noma da kuma daukar wasu zuwa horo a IITTA.

Manoman na Neja sun kuma yabawa kokarin Gwamna Bago wajen aiwatar da manufofin da suka ingantar harkar noma, wadanda suka kawo sauyi a jihar

Dalilin saya wa Gwamna Bago fam

Mataimakin sakataren kudi na kungiyar masu kiwon kaji kuma mataimakin shugaban AFAN a jihar Neja, Mohammed Saba Usman, ya ce sun sayi fom din ne domin nuna godiya ga ayyukan da shugabannin suka yi a bangaren noma.

Ya ce:

“Mun yi nazari kan ayyukan da aka mana, kuma mun ga sauyi mai yawa a harkar noma a jihar Neja, wanda manomin gwamna ya fara, tare da hadin kan Hon. Sa’idu Musa Abdullahi.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni da 'yan APC sun fitar da dan takarar gwamnan Yobe a 2027

“Wannan lokaci ne na rama alheri. Sun yi kokari sosai wajen samar da kayan aiki, taki, taraktoci da kuma bunkasa amfanin gona, wanda ya samar da ayyukan yi ga mutane da dama.”
APC .
Tutar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya Hoto: @Officia'APCNig
Source: Twitter

Usman ya kara da cewa tun bayan kafuwar jihar Neja a 1976, ba a taba samun gwamna da ya bai wa noma muhimmanci kamar Bago ba, cewar rahoton Daily Post.

Minista zai nemi takarar gwamnan Neja?

A wani labarin, kun ji cewa ministan yada labarai, Mohammed Idris ya karyata rahotannin dake cewa zai shiga yakin neman takarar gwamnan Neja a zaben 2027.

Idris ya nesanta kansa da wani rubutun siyasa da ke yawo a kafafen yaɗa labarai mai taken “Malagi 2027,” da hadiminsa, Sa'idu Enagi ya wallafa.

Ministan ya nanata cewa ra’ayoyin da aka bayyana a rubutun ba su wakiltar matsayinsa ko manufofinsa na siyasa, don haka ya yi kira ga daukacin jama’a da su yi watsi da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262