Farashin Fetur Ya Tashi a Najeriya, ana Fargabar Lita za Ta kai N1500

Farashin Fetur Ya Tashi a Najeriya, ana Fargabar Lita za Ta kai N1500

  • Farashin man fetur na cigaba da cillawa sama yayin da Shugaban Amurka, Donald Trump da Iran suka gaza cimma mastaya kan Hormuz
  • Matatar Dangote da ke tace man fetur da sauransu a Najeriya ta kara kudin mai, lamarin da ya jawo hauhawar farashi a fadin kasar
  • Masana sun yi hasashen litar fetur za ta iya kai wa N1500 matukar ba a cimma matsayar kawo zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Farashin litar man fetur a gidajen mai ya doshi N1,400 a sassa da dama na kasar nan, yayin da Amurka da Iran suka kasa cimma yarjejeniyar da za ta sa a bude mashigar Hormuz.

Yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba, tare da ficewar Hadaddiyar Daular Larabawa daga kungiyar OPEC a ranar Talata, farashin fetur na ci gaba da hauhawa.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya dauki bindiga yana yi wa Iran sabuwar barazana

Ana sanya fetur a wata mota
Wani mai mota na sayen fetur a gidan mai a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yadda farashin mai ya tashi

Rahoton da tashar BBC ta wallafa ya nuna cewa daga $105 a kan kowace ganga a ranar Litinin, farashin Brent ya tashi zuwa $118 a ranar Laraba.

Sakamakon haka, matatar Dangote ta kara farashin fetur daga N1,200 zuwa N1,275, lamarin da ya kara dagula lamura a Najeriya.

Wata majiya ta ce matatar ta dakatar da tsarin shigar da takardun sayen mai da misalin karfe 4:00 na yammacin Talata, lamarin da ya kawo tsaiko a jadawalin lodin mai.

An bayyana cewa wannan na iya nuni da cewa matatar Dangote za ta kara kashe kudi wajen sayen danyen mai, wanda hakan zai iya janyo karin farashin mai a kasuwa.

Farashin fetur a gidajen mai

An lura cewa gidajen mai sun gaggauta kara farashi daga kusan N1,250 zuwa sama da N1,300 a Lagos da wasu jihohin Kudu maso Yamma.

Bincike ya nuna cewa a Lagos da Ogun, ana sayar da fetur tsakanin N1,315 zuwa N1,350. A wasu gidajen mai na NNPC a hanyar Mowe/Ibafo, ana sayar da fetur a N1,315, yayin da Mobil ke sayarwa a N1,320.

Kara karanta wannan

Kamfanin NNPCL ya sauya farashin mai saboda yakin Iran da Amurka

Farashin na bambanta gwargwadon wuri. A Arewa da sauran yankunan da ke nesa da matatar Dangote, farashin ya kai kusan N1,400 a lita.

A wasu yankunan kan iyakar Ogun, mazauna sun ce farashin ya kusa kaiwa N1,700 saboda rashin isar da mai yadda ya kamata.

Mutane na sayen mai a gidan mai
Yadda ake sayen man fetur a gidan mai a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bayanin masani kan tsadar mai

Shugaban kungiyar masu gidajen sayar da man fetur (PETROAN), Billy Gillis-Harry, ya ce farashin na iya ci gaba da tashi idan har ba a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba.

Ya kara da cewa sauyin farashi cikin gaggawa na sa kasuwanci ya zama mai wahala ga ‘yan kasuwa, yana mai korafin cewa gwamnati ba ta daukar matakan tallafawa jama’a duk da karin kudin shiga da take samu daga tsadar mai.

Rahoton Punch ya nuna cewa ya kuma gargadi cewa farashin fetur na iya haura N1,500 a lita idan rikicin Gabas ta Tsakiya bai lafa ba.

Najeriya ta kara farashin mai

A wani labarin, mun kawo muku cewa kamfanin man Najeriya na NNPCL ya kara farashin sayar da danyen mai da ake fitarwa zuwa ketare.

Kara karanta wannan

OPEC+: UAE ta dauki mataki 1 da ya girgiza Saudiyya da kasuwar mai ta duniya

Rahoto ya nuna cewa Najeriya na cin gajiyar rikicin Amurka da Iran, inda ta kara farashin Bonny Light da $6.13, yayin da Forcados ya karu da $7.01.

Sanarwar da aka fitar ta nuna cewa sabon farashin zai fara aiki daga gobe Juma'a, 1 ga watan Mayun 2026, wanda aka ce zai shafi rayuwar 'yan kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng