Magana Ta Ƙare: Tsohon Gwamna da Ƴarsa Kwamishina Sun Watsar da PDP Zuwa APC

Magana Ta Ƙare: Tsohon Gwamna da Ƴarsa Kwamishina Sun Watsar da PDP Zuwa APC

  • APC ta dada samun ƙarfi da tsohon gwamnan Delta, Dr. Emmanuel Uduaghan, ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar a gidansa da ke Warri
  • Jiga-jigan jam'iyyar APC sun tarbe shi, ciki har da shugabar mata ta yankin Delta ta Kudu, Alero Tenumah, da shugaban mazabar Abigborodo
  • ’Yarsa, Orode, kwamishiniyar jin ƙai ta jihar, ita ma ta karɓi katin APC, tana goyon bayan muradun Bola Tinubu da Gwamna Sheriff Oborevwori

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Warri, Delta - Jam'iyyar APC ta sake gigita jam'iyyun adawa bayan karɓar tsohon gwamna zuwa cikinta.

Tsohon Gwamnan jihar Delta, Dr. Emmanuel Uduaghan, ya tabbatar da kasancewarsa ɗan jam’iyyar APC a hukumance.

Tsohon ya PDP zuwa APC
Tsohon gwamnan Delta ya koma APC. Hoto: Emmanuel Uduaghan, Orode Uduaghan.
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Uduaghan ya yanki katin jam'iyyar a gidansa da ke Warri a jihar Delta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda jam'iyyar APC ta wargaza PDP a Delta

APC ta kwashe kusan kowa a jihar Delta a makon da ya gabata bayan dukan mukarraban gwamnati sun bar PDP.

Daga cikinsu akwai gwamnan jihar, Sheriff Oborevwori da mataimakinsa da yan majalisu da kuma kwamishinoninsa.

Har ila yau, tsohon gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa shi ma ya tsere daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Okowa shi ne ya yi mataimaki ga Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa da aka gudanar a shekarar 2023.

Tsohon gwamna ya koma APC
Tsohon gwamnan Delta da ƴarsa sun koma APC. Hoto: Emmanuel Uduaghan, Orode Uduaghan.
Asali: Facebook

Tsohon gwamna ya bar PDP zuwa APC

Dr. Uduaghan ya karɓi katin zama ɗan APC a ranar Litinin wanda ya nuna shigarsa jam’iyyar a hukumance.

An tarbe shi da hannu bibbiyu daga shugabannin jam’iyya ciki har da shugabar mata ta APC Delta ta Kudu, Alero Tenumah da George Ino na mazabarsa.

Yayin da yake nuna sabon katinsa mai lamba Delta WRN//023/32001, Uduaghan ya gode bisa tarbar da aka yi masa tare da alƙawarin aiki don ci gaban Delta.

Ƴar tsohon gwamna kuma kwamishina ta koma APC

A cikin wata alama da ke kara nuna goyon baya, ’yarsa Orode Uduaghan ita ma ta bi sahun mahaifinta.

Orode wacce ita ce kwamishiniyar jin ƙai ta jihar ta karɓi katin APC daga shugabannin yankin don ba da gudunmawa ga jam'iyyar.

Alero Tenumah ta ƙarfafawa sababbin mambobi su karɓi katinsu, su mara baya ga shirin Tinubu na “Renewed Hope” da manufar Gwamna Oborevwori ta M.O.R.E.

Ta tabbatar wa Dr. Uduaghan da haɗin gwiwa mai amfani domin ƙarfafa jam’iyyar a Karamar Hukumar Warri ta Arewa da sauran sassan jihar.

Hadimin gwamnan Delta ya yi murabus

Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Delta ta fuskanci koma baya, Harrison Gwamnishu, mai ba gwamna shawara kan matasa da kungiyoyin farar hula, ya ajiye aikinsa.

Matashin dan siyasar ya bayyana a wasikar murabus dinsa cewa duk kokarinsa na shawo kan Gwamna Oborevwori game da matsalar tsaro da ya ci tura.

A cewarsa, rashin yanke shawara mai ma’ana daga gwamnati ya sa ya kasa ci gaba da aiki da amana da nagarta kamar yadda ya yi alkawari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.