"Dole Ta Sa Na Nemo Mafita," Bola Tinubu Ya Faɗi Kuɗin da Buhari Ya Bari a Baitul Mali
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ya gaji baitul-malin da babu isassun kuɗi kuma ga tarin matsaloli a lokacin da ya karɓi mulki a 2023
- Tinubu ya bayyana cewa ya gaji basussuka, tallafin da ya wuce gona da iri, da tsarin musayar kuɗi da ya zama alaƙaƙai ga tattalin arziki
- Shugaban ƙasar ya ce matakan da ya ɗauka sun zama dole domin farfaɗo da tattalin arziki da kuma gina tubalin ci gaba mai ɗorewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gaji “baitul-mali cikin mawuyacin hali” a fannin tattalin arziki da tsarin musayar kuɗi a 2023.
Shugaba Tinubu ya ce lokacin da ya karɓi mulki a watan Mayu, 2023, ya tarar da lalitar gwamnati kusan babu ko kwandala da kuma tarin matsaloli.

Asali: Twitter
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a wata ziyarar aiki da taron girmamawa da aka shirya masa a Awka, babban birnin Jihar Anambra, cewar Tribune Nigeria.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubuwan da Tinubu ya tarar a baitul-mali
Shugaban kasar ya ce lokacin da ya hau mulki, kasar na fama da dimbin basussuka, tallafin da ba za a iya jurewa ba, da tsarin musayar kudade mara kan-gado.
“Mun gaji kudi ƴan kaɗan a lalitar gwamnati, mun gaji tallafin da ya jima yana laƙume dukiyarmu, da kuma tsarin musayar kudi mai cike da rudani,” in ji Tinubu.
Duk da radadin da talakawa ke fuskanta sakamakon cire tallafin mai da kuma faɗuwar darajar Naira, Tinubu ya jaddada cewa tsare-tsaren da ya kawo sun zama dole a halin da ya tsinci ƙasar.
Bola Tinubu ya nemi ƴan Najeriya su jure
A cewarsa, zuwa yanzu matakan da ya ɗauka na cire tallafi da sauran makamantansu, sun fara haifar da ɗa mai ido ga tattalin arzikin ƙasa.
"Waɗannan tsare-tsaren sun kawo ƙunci da wahala amma babu yadda muka iya, ba za mu iya kauce masu ba."
"Karfin hali, juriya da hadin kan kowa ake bukata don mu gyara, mu kuma gina tushe mai karfi don samun ci gaba mai dorewa.”
- Bola Tinubu.
A ziyararsa ta farko zuwa Anambra tun bayan darewarsa kan karagar mulki, Shugaba Tinubu ya kaddamar da wasu manyan ayyukan ci gaba da Gwamna Charles Soludo ya kammala.
Daga cikin ayyukan da ya ƙaddamar akwai wurin yawon buɗe ido da shaƙatawa, 'Solution Fun City' da sabon gidan gwamnatin jihar da aka gina, rahoton Punch.

Asali: Twitter
Gwamna Soludo ya sha yabo daga Tinubu
Shugaban kasar ya yabawa ƙoƙarin Gwamna Soludo na mayar da jihar Anambra “tamkar Dubai, Taiwan, da Silicon Valley,” na nahiyar Afirka.
Tinubu ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da goyon bayan Anambra a fannonin tsaro, gina ababen more rayuwa, da kuma inganta fasaha da masana’antu.
Tinubu ya nemi fili a Anambra
A wani rahoton, kun ji cewa Bpla Tinibu ya ce wataƙila ya nemi filin da zai gina gidan da zai yi rayuwa bayan ya yi ritaya a jihar Anambra.
Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa na aiki tare da Gwamna Soludo domin ci gaban jihar Anambra da warware matsalolin da suka addabi al'umma.
Shugaban kasa Tinubu ya bayyana jin dadinsa da irin ci gaban da aka samu a jihar, inda cikin raha ya bukaci Soludo da ya samo masa fili.
Asali: Legit.ng