NNPP: Barau Ya Kwashe 'Yan Kwankwasiyya zuwa APC a Dukkan Shiyyoyin Kano

NNPP: Barau Ya Kwashe 'Yan Kwankwasiyya zuwa APC a Dukkan Shiyyoyin Kano

  • Gungun matasa, mata da dattijai daga dukkan shiyyoyin Kano uku sun sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC
  • Shugabar mata ta NNPP a Dakata, Fatima Abubakar ta jagoranci mabiyanta wajen barin jam’iyyar mai mulki a jihar Kano
  • Sanata Barau Jibrin ya yaba da matakin nasu tare da basu tabbacin samun dama daidai da kowa a jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Wasu gungun 'yan Kwankwasiyya da jam’iyyar NNPP a Kano sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Sun bayyana haka ne bayan wani taro da aka gudanar a ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, a Abuja.

Barau
Barau ya karbi tarin 'yan NNPP zuwa APC a Abuja. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

'Yan NNPP sun bi Barau zuwa APC

A sakon da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a X, ya bayyana cewa wadanda suka sauya shekar sun fito ne daga shiyyoyi uku na jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Barau ya karbi bakuncin gungun mutanen a ofishinsa da ke majalisar tarayya tare da rakiyar manyan jam’iyyar APC.

Kwamishinan hukumar kula da harkokin majalisa ta kasa, Yusuf Tabuka, da kwamishinan hukumar tsara albashi ta kasa (RMAFC), Adamu Fanda sun halarci taron.

A cewar wadanda suka sauya shekar, ayyukan da Sanata Barau da APC ke aiwatarwa a Kano ne suka jawo su, tare da fatan ci gaba da aiki don bunkasa jihar da kasa baki daya.

Mata da matasa sun rungumi APC A Kano

Daya daga cikin muhimman wadanda suka sauya sheka ita ce shugabar mata ta jam’iyyar NNPP a unguwar Dakata, Fatima Abubakar,.

Fatima Abubakar ta jagoranci dimbin mabiya wajen komawa APC kuma ta bayyana cewa ta gamsu da salon shugabanci da kuma damarmakin ci gaba da APC ke bayarwa.

Sauya shekar ta nuna karfin da APC ke ci gaba da samu a jihar Kano, musamman daga tsofaffin magoya bayan NNPP da suka dade suna mara baya ga tafiyar Kwankwasiyya.

Sanata Barau ya yi maraba da 'yan NNPP

Sanata Barau Jibrin, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawa, ya bayyana jin dadinsa da matakin da wadannan kungiyoyi da daidaikun mutane suka dauka.

Ya kuma tabbatar musu da cewa za su samu daidaito da duk wani dan jam’iyyar APC wajen samun dama da ci gaba, tare da bukatar su ci gaba da jajircewa wajen raya jihar Kano.

Barau
Barau ya bukaci hadin kai bayan karbar 'yan NNPP. Hoto: Barau I Jibrin
Asali: Facebook

Sanata Barau ya bukaci hadin kai a APC

Sanatan ya bukaci sababbin mambobin jam’iyyar da su kasance masu aiki tukuru da sadaukar da kai domin ganin an cimma nasarar jam’iyyar a gaba.

Barau ya kuma jaddada cewa APC za ta ci gaba da karfafa gwiwar sababbin mambobinta ta hanyar basu cikakken tallafi da dama a harkokin siyasa da ci gaban al’umma.

Manyan APC sun yi wa Tinubu mubaya'a

A wani rahoton, kun ji cewa masu magoya bayan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari sun jaddada goyon baya ga Bola Tinubu da APC.

Magoya bayan Buhari da suka yi aiki tare a tsohuwar jam'iyyar CPC sun bayyana haka ne yayin wani taro a Abuja.

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda da wasu tsofaffin gwamnoni da manyan jami'an gwamnati sun halarci taron.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng