Shugaban Malamai a Izala, Sheikh Saidu Hassan Jingir Ya Rasu
- Rahotanni na nuni da cewa mataimakin shugaban malaman kungiyar Izala na kasa na biyu, Sheikh Saidu Hassan Jingir, ya rasu
- Sheikh Saidu Hassan Jingir ya shafe shekaru yana karantar da addini a jihohi da dama kafin Allah Madaukakin Sarki ya masa rasuwa
- Za a yi jana'izarsa da misalin karfe 2:00 na rana bayan sallar Azahar a masallacin Santa, Unguwar Rimi a jihar Filato a yau Alhamis
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato - Allah ya yi wa Sheikh Saidu Hassan Jingir, mataimakin shugaban malaman Izala na kasa na biyu, rasuwa.
Rahotanni sun nuna cewa Sheikh Saidu Hasssan Jingir ya rasu ne bayan jinya da ya dade yana fama da ita.

Asali: Facebook
Dan agajin Izala, Hamza Muhammad Sani ne ya sanar da rasuwar malamin a shafinsa na Facebook, inda ya roki Allah ya gafarta masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bayyana cewa za a yi jana’izar marigayin a masallacin Santa da ke Unguwar Rimi, kusa da gidan Sheikh Jingir.
Gwagwarmayar Sheikh Jingir a Izala
Sheikh Saidu Hassan Jingir ya na daga cikin jiga-jigan da suka taka rawa a kungiyar Izala a Najeriya.
Malamin ya shafe shekaru da dama yana wa’azi da karantar da jama’a a sassa daban-daban na kasar nan.
A baya, ya rike mukamin mataimakin shugaban malaman Izala na daya kafin hadewar kungiyar, daga baya aka ba shi na biyu.
Sheikh Jingir ya kasance daya daga cikin malamai masu tasiri a harkar wa’azi da yada addinin Musulunci.
Jingir: Shahararren malami mai tafsiri
A lokacin rayuwarsa, Sheikh Saidu Hassan Jingir ya gudanar da tafsiri a jihohi da dama a fadin Najeriya.
Haka zalika wa’azinsa ya shahara musamman a jihohin Arewa, inda jama’a da dama ke amfana da iliminsa.
An bayyana cewa ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya da ya yi a kwanakin baya duk da cewa ya dan samu sauki kafin rasuwarsa.
Rasuwar Sheikh Saidu Hassan Jingir ta girgiza al’ummar musulmi, inda mutane ke nuna alhinin wannan babban rashi.
Al’umma sun yi alhinin rashin Sheikh Jingir
Bayan sanar da rasuwarsa, al’umma daga ciki da wajen Najeriya sun nuna alhininsu a kafafen sada zumunta.
Sheikh Jingir yana da dimbin mabiya da suka rika wallafa addu’o’i da jajantawa danginsa da almajiransa.

Asali: Facebook
Lokacin jana'izar Sheikh Saidu Jingir
Kungiyar Izala mai hedkwata a Jos ta bayyana cewa za a yi jana’izar malamin da misalin karfe 2:00 na rana bayan sallar Azahar a masallacin Santa da ke Unguwar Rimi a jihar Filato.
Ana sa ran mutane da dama daga ciki da wajen jihar Filato, musamman malamai za su halarci jana’izar malamin domin yi masa girmamawar karshe.
Sheikh Guruntum ya bude sabon masallaci
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya bude sabon masallaci a jihar Bauchi ana daf da fara azumin Ramadan.
Rahotanni sun nuna cewa an shafe shekaru ana gina katafaren masallacin kuma tuni an fara gudanar da tafsirin azumin 2025 a masallacin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng